Duba hotunan ban mamaki na wata mace da siffan Ayu tana iyo a cikin ruwan Glasgow - isyaku.com


Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi sanadin malalewar unguwanni a karsar United Kingdom UK, lamari da ya sa magudanan ruwa suka cika har suka batse. Sakamakon haka mutane ke ta kokarin ganin sun taimaka wa kansu bisa wannan dalili. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.

Ana cikin haka ne, wani mazauni Glasgow, wanda har yanzu ya kasa ficewa daga gidansa sakamakon ambaliyar ruwan, ya gano wani abin mamaki..Gavin Millar, ya dauki hotunan wata mata mai siffan Ayu tana iyo a cikin ruwan. Ya dauki hoton ne daga kan benen gidasa da ke Battlefield Gardens, wanda ke sashen kudancin birnin Gasgow ranar 7 ga watan Agusta.

Sai dai daga bisani an gano cewa wata mace ce ta saka rabin tufan Zabaya tana iyo domin a dauketa hoto.


 

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN