Duba dalilin da ya sa Hisbah ke so a cire kan ƴar tsanar tallar kaya a shaguna



Hukumar Hisbah a jihar Kano mai yawan Musulmi a Najeriya ta janyo ce-ce-ku-ce bayan da ta umarci shaguna su cire kawunan ƴar tsanar da ake mafni da ita wajen tallar kayan sawa.

"Musulunci ba ya son mu'amala da gumaka," kamar yadda Haruna Ibn-Sina, shugaban hukumar ya shaida wa BBC.

"Idan aka bar kan ƴar tsanar a jikinta, tana kama da mutum," a cewarsa.

Ibn-Sina na so a riƙa rufe ƴar tsanar da aka cire wa kai ta zama a lulluɓe a ko yaushe saboda "surar mama da mazaunai da ke jikin ƴar tsanar ya saɓa wa dokar addinin Musulunci na Shari'a".

Kano na ɗaya daga cikin jihohi 12 na arewacin Najeriya masu rinjayen Musulmi. Ya kamata a ce tsarin shari'ar na aiki ne kan Musulmi kawai.

Amma a zahiri, waɗanda ba Musulmi ba na fuskantar matsin lambar su bi dokokin, ciki har da hana amfani da ƴar tsanar ta tallar kaya mai kai.

"Mun samu kiraye-kiraye da saƙonni da dama daga mutanen da ba su amince da umarnin ba," in ji Moses Ajebo, wani mai gabatar da shirye-shirye a birnin Kano, birni na biyu mafi girma a Najeriya.

Haruna Sina and entourage

Bayanan hoto, Kwamanda Ibn-Sina (sanye da korayen kaya) na yawo da tawagarsa

Ƴan kasuwa a Sabon Gari, wani ɓangare na jihar da mafi yawan mazaunanasa Kiristoci ne, sun nuna rashin jin daɗinsu kan umarnin na Hisbah.

Wani mai shago Chinedu Anya ya ce tallar kaya a kan ƴar tsana marar kai zai rage kyawun kayan ga masu wucewa kuma wannan zai shafi sana'arsa.

An yi wa matasa aski

Ibn-Sina da dubban jami'ansa maza da mata - ba su riga sun fara bi shago-shago suna tabbatar da an fara aiki da umarnin ba.

Sai dai akwai fargabar cewa wannan umarni ta shiga jerin dokokin Hisbah da ke cin karo da bambancin addinai da ci gaba.

A makon da ya gabata ne Ibn-Sina ya soki hotunan bikin Zahra Bayero, matar ɗan shugaban Najeriya, Yusuf Muhammadu Buhari.

Ya ce ba ta nuna misali mai kyau ga sauran Musulmi ba saboda ta ɗauki hoton kafaɗarta a bayyane.

Karshen labarin da aka sa a Facebook, 1

1px transparent line

Ya kuma so wadanda suka riƙa yaɗa hotunan inda ya ce zunubi na kansu.

Bara ne jami'an hukumar ta Hisbah suka aske wa wasu matasa gashin kansu saboda irin askin nan na zamani da ake tara gashi a saman kai da suka yi a birnin na Kano, kuma ya soki masu zazzago wandunansu zuwa ƙasan kwankwanso.

Haka kuma, Ibn-Sina ya haramta amfani da kalaman 'Black Friday' a lokacin tallar kaya inda ya ce ranar Juma'a rana ce mai tsarki a Musulunci.

Tashoshin rediyo da manyan kantuna da dama sun yi burus da gargaɗin nasa kuma bai yi masu wani hukunci ba.

Ya yi wa mazauna garin gargaɗi kan yin wata rawa ta Afrika ta Kudu - inda masu yin ta ke faɗuwa ƙasa a cikin rawa- wadda ta yi tashe a bara.

Yayin da Musulmi da yawa a Kano ke goyon bayan umarnin Hisbah, wasu matasa na ganin yadda hukumar ke kallon wasu dokokin addinin Musulunci kamar na ƴar tsanar tallan kaya ba dai-dai ba ne.

"Musulunci ya hana amfani da gunki amma hadisin Annabi ya bayyana cewa Allah na aiki da niyya ce. Matsawar ba sujjada kake yi wa ƴar tsanar ba, amfani da ita bai zama zunubi ba," a cewar wani Malamin addini da ba ya so mu bayyana sunansa.

Duk da cewa sanarwar ta Kano irinta ce ta farko a Najeriya, an yi irin wannan yunƙurin a wasu ƙasashen duniya na Musulmi.

A 2009, yan sanda a Iran sun gargaɗi masu shago kan bayyana yar tsanar mai surar mace ba tare da sa mata hijabi ba.

Headscarves are displayed on mannequins at the Islamic fashion exhibit in central Tehran on December 18, 2014.

Bayanan hoto, A Musulunci dole ne mace ta rufe gashin kanta

A 2010, ƙungiyar Hamas mai ikirarin jihadi a Falasɗinu ta umarci cire ƴar tsanar da hotunan masu tallar kayan ƙawa da ke sanye da ɗan wando da rigar mama daga shaguna a Zirin Gaza.

A lokacin, Hamas ta ce sun sa dokar ne don ta tsarkake al'umma.

Amma ga mutanen Kano, babu tabbas kan yadda za a tabbatar da amfani da dokar tunda Malam Ibn-sina ya ce ba zai ƙwace yar tsanar masu saɓawa ba, inda ya ce ya fi so ya bi "wasu hanyoyin".

Malamin addinin Musulunci, Malam halliru Maraya na so waɗanda ba Musulmi ba da kundin tsarin mulkin Najeriya ya kare su ƙalubalanci umarnin hukumar ta Hisbah kan amfani da yar tsanar inda ya ce ya kamata a ja layi kan tursasa masu amfani da dokokin Musulunci.

Amma yin adawa da Hisbah na iya nufin shiga mawuyacin hali.

An zubar da ruwan giya

Sama da mutum 100 aka kashe a wani jerin zanga-zanga da aka gudanar don nuna kin jinin matakin gwamnatin jihar Kano na fara amfani da dokar Shari'a shekaru 11 da suka gabata.

A baya-bayan nan, Hisbah ta lalata wasu manyan motoci ɗauke da kwalaben giya na wani wanda ba Musulmi ba kuma ta far wa shagunan sayar da barasa bayan da ta zargi masu kayan da aikata "laifukan da ba su dace ba."

A Musulunci an haramta shan giya.

Hisbah officers destroying alcohol

Bayanan hoto, Hisbah na ƙwacewa da lalata barasa da sauran kayan maye waɗanda aka haramta sha a Musulunci

Hukumar hisba ta Kano ba ta da maraba da ta sauran jihohin Najeriya masu rinjayen Musulmi. Amma ta fi sauran yin suna saboda Malam Ibn-Sina.

Waɗanda suka san shi sun ce mutum ne shi mai son nuna kansa kuma yana da son a san da shi. Ya kan zagaya birnin Kano tare da ƴan jarida suna mara masa baya don bayar da umarni.

Amma ya ce shi aikinsa kawai ya ke yi.

Bara, kwamandan ya janyo ce-ce-ku-ce lokacin da ya yi hayar wasu ƙwararru a ɓangaren damben Kung Fu don horar da jami'an hukumarsa.

An yi ta yayata wannan, kuma ga mutanen garin hakan ya zama abin dariya.

Ga ƴar tsanar tallar kaya kuwa, mai yiwuwa ƙarshenta ya zo a Kano. Sai dai kawo yanzu ba a sani ba ko wani abin zai ɗauke hankalin Malam Ibn-Sina.

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN