Duba dalili da ya sa aka kai dan gidan Yar'Adua gidan Kurkuku


Wata kotun majistiret da ke Yola babban birnin jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya ta kai Aminu Yar'Adua, dan gidan marigayi shugaban kasa Umaru Musa Yar'Adua, gidan yari. BBC Hausa ta ruwaito.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya rawaito cewa kotun ta aika da matashin, mai shekara 36, gidan maza ne bisa zarginsa da kisan mutum hudu yayin wani hatsarin mota da ya auku a birnin Yola.

Aminu Yar'Adua, dalibi ne a Jami'ar American University of Nigeria (AUN) Yola, kuma kotun tana zarginsa ne da yin tukin ganganci ranar 23 ga watan Yunin 2021.

Sai dai ya musanta zargin yana mai cewa babu kanshin gaskiya a cikinsa.

A cewar takardar shigar da kara da dan sanda mai gabatar da kara, Zakka Musa, ya mika wa gaban kotun, ana zargin Aminu Yar'Adua da buge mutum shida yayin tukin ganganci a kan babban titin Yola.

Kotun ta ji cewa mutum hudu daga cikinsu sun mutu yayin da biyu suka samu raunuka, tana mai cewa mutanen sun fito ne daga yankin Sabon Pegi da ke Karamar Hukumar Yola Ta Kudu.

"Mutanen da suka mutu lokacin hatsarin su ne; Aisha Umar (mai shekara 30), Aisha Mamadu (mai shekara 32), Suleiman Abubakar(dan shekara biyu) da kuma Jummai Abubakar (mai shekara 30), yayin da kuma Rejoice Annu (mai shekara 28) da Hajara Aliyu (mai shekara 27) suka ji raunuka," a cewar takardar shigar da kara.

Alkaliyar kotun, mai shari'a Jummai Ibrahim, ta É—age sauraren karar zuwa ranar 19 ga watan Agustan 2021, inda ya bayar da umarni a kai Aminu Yar'Adua kurkuku kafin lokacin.

Dan sanda mai shigar da kara ya shaida wa kotun cewa iyalan marigayiya Aisha Umar da Jummai Abubakar da kuma marigayi Suleiman Abubakar sun bukaci a biya su N15m a matsayin diyya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN