Duba abinda ya faru har yan fashin daji 78 suka mutu nan take a jihar Zamfara


Rundunar sojin saman Najeriya ta ce jiragen yakinta sun yi luguden bama-bamai a kan sansanonin 'yan fashin daji cikin jihar Zamfara - har ma sun kashe aƙalla saba'in da takwas. BBC Hausa ta ruwaito.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar, sojojin saman na Najeriya sun ce wasu daga cikin 'yan fashin dajin kuma sun tsere yayin samamen.

Ta ce hadin gwiwar dakarun tsaron sun kwashe tsawon kwana uku tun daga ranar Litinin har zuwa Laraba suna lugude a kan 'yan fashin dajin - waÉ—anda suka addabi yankin.

A cewar rundunar luguden bama-baman ya shafi sansanonin 'yan fashin dajin da ke cikin dajin Kuyanbana, kudu da garin Ɗan Sadau cikin ƙaramar hukumar Maru.

Zamfara na cikin jihohin da suka fi fama da hare-haren 'yan fashin daji a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya, waÉ—anda ke cin karensu babu babbaka a sassa da dama na jihohin Neja da Zamfara da Kaduna da Sokoto da Katsina da kuma Kebbi.

Rundunar sojin saman Najeriya dai ta ce yayin wannan artabun sojoji na kwana uku, an yi amfani da jiragen yaƙi iri daban-daban don tarwatsa sansanonin 'yan bindigar.

Ta ce wasu daga cikin 'yan fashin dajin ma, an kashe su ne a lokacin da suke ƙoƙarin tserewa a kan babura, duk da yake, akwai wasu a cikinsu da suka tseren.

Haka zalika, an lalata sansanoni da dama na 'yan fashin daji da ke cikin dajin na Kuyanbana, a cewar rundunar sojin saman Najeriya.

Sojojin sun kuma ce a wani lokaci sai da aka yi amfani da tallafin sojojin ƙasan Najeriya wajen yi wa 'yan bindigar ƙofar rago da kuma datse hanyoyinsu na tserewa.

Samamen dai ana iya cewa shi ne na baya-bayan nan da haɗin gwiwar sojojin sama da na ƙasan Najeriya ke kai wa don murƙushe ɓarayin dajin a shiyyar arewa maso yamma

Wakilin BBC Ishaq Khalid ya ruwaito cewa farmakin sojan na zuwa ne daidai lokacin da hukumomin ƙasar ke ci gaba da shan suka saboda abin da 'yan Najeriya da dama ke cewa gazawarsu wajen shawo kan tashin hankalin da 'yan fashin daji ke haddasawa.

"Musammam ma sace-sacen mutane da kai hare-haren da kan janyo mutuwar al'ummomi a yankunan karkara cikin shiyyar arewa maso yammacin ƙasar," in ji Ishaq.

Ya ce a 'yan watannin baya-bayan nan an sace É—umbin mutane cikinsu har da É—alibai fiye da 1,000 waÉ—anda akan je har makarantunsu a sassa daban-daban a yi awon gaba da su.

"Ko da yake, an sako wasu daga cikinsu amma har yanzu akwai kimanin 300 da ke can a hannun 'yan fashin da ke tsakiyar daji," cewar wakilin na BBC.

Ya ce matsalar 'yan fashin daji tana ci gaba da addabar al'ummar ƙasar, inda a cikin shekarun baya-bayan nan dubban mutane suka mutu sanadin wannan tashin hankali.

"Yayin da hukumomi kuma suka ci gaba da shan suka da kuma zarge-zargen na rashin kataɓus, amma wannan samamen soja a baya-bayan nan, da suke iƙirarin sun kashe gomman 'yan fashin daji ka iya zama wani abin bugun ƙirji ga hukumomin Najeriya".

Jami'an tsaron Najeriya dai ciki har da rundunar sojin sama da ta ƙasa sun zafafa farmakin da suke kai wa ƴan bindiga masu kai munanan hare-hare tare da sace-sacen mutane don kuɗin fansa a yankin na Zamfara a baya-bayan nan.

Ƴan bindiga sun sace sama da ɗalibai 1000 daga makarantunsu tun daga watan Disamban da ya wuce kawo yanzu.

Har yanzu, akwai kusan É—alibai 300 a hannun yan bindiga.

Hukumomin Najeriya na shan suka kan gazawarsu wajen kawo ƙarshen ayyukan ƴan fashin daji da masu satar mutane.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN