Duba abinda ya faru bayan Malam Abduljabbar Nasir Kabara ya sake gurfana kotu


Malam Abduljabbar Nasir Kabara ya sake gurfana gaban kotu a Kano kan laifukan da ake tuhumarsa na yin kalaman tunzura jama'a da ɓatanci ga addinin Islama. Zargin da ya sha musantawa,  BBC Hausa ta ruwaito a shafinta.

A ranar 30 ga watan Yulin da ya gabata aka fara gurfanar da Abduljabbar Nasir Kabara, inda aka gabatar da takardar korafin farko.

Gwamnatin Kano ta ce ta gurfanar da Malamin ne, wanda ta ce ya yi ƙaurin suna wajen yin wa'azin da kan haifar da mahawara, saboda zargin furta kalaman da ka iya haifar da tunzuri, da kuma bata sunan Annabin Allah''.

Wakilin BBC da ke cikin kotun da ake sauraren ƙarar Malam Abduljabbar ya ce an tsaurara tsaro fiye da zaman kotun da aka yi a farko.

Ya kuma ce Malam Abduljabbar a ya rame a yanayin yadda ya bayyana a sauraren ƙararsa da ake yi a kotun a ranar Laraba.

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari