Duba abin da yan Taliban suka yi wa dan Luwadi a Afghanistan


Yan Taliban a kasar Afghanistan sun yi wa wani dan Luwadi dan karen duka bayan sun lallashe shi ya fito daga wajen da ya boye. Yan Taliban sun nuna masa cewa su yan harkar ne da ke shirin bashi kariya domin ya fice daga kasar. Sai dai bayan da ya fito sai suka kama shi suka yi masa dukan tsiya. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.

Wannan na zuwa ne bayan kasar Amurka ta kammala kwashe sojinta daga kasar Afhanistan ranar Laraba 31 ga watan Agusta.

Dan karadin kare hakkin dan adam Artemis Akbary, ya shaida wa gidan Talabijin na ITV a kasar Tukiyya lamari da ya faru da dan luwadin.

Ya kuma yi zargin cewa yan Taliban na tilasta yara mata kanana yan shekara 12 auren mayakan Taliban ko suna so ko basa so.

Ya ce har yanzu dai akidar nan ta yan Taliban bata canja ba tsawon shekara 20 da Amurka da kawayenta suka yakar akidar.

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari