Daya daga cikin yan matan Chibok ta dawo gida bayan shekara 7 da sace su, ta gana da Gwamna Zulum

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya karbi daya daga cikin yan matan Chibok a gidan Gwamnati ranar Asabar 7 ga watan Agusta. Ruth Ngladar Pogu, tana daya daga cikin yan matan makarantar Sakandare na Chibok su dari 200 da yan Boko haram suka sace shekara 7 da suka gabata, Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.

Idan baku manta ba, ranar 14 ga watan Aprilu,  2014, da tsakar dare yan Boko haram suka dira makarantar mata na Chibok kuma suka yi awon gaba da yan mata da dama.

Wata sanarwa daga gidan Gwamnatin jihar Borno ta ce Ruth, tare da wani wanda aka aurar da ita ala tilas gareshi, sun mika kansu suka yi saranda ga sojin Najeriya ranar 28 ga watan Yuli 2021 a wani wuri a cikin garin Bama

Sai dai Gwamnati ta sirrinta lamarin har sai da aka tantance tare da tabbatar da iyayenta har tsawon kwana 10, kafin aka tabbatar cewa Ruth ce wacce yan Boko haram suka tilasta ta auren wani dan kungiyar, wanda yana daya daga cikin yan Boko haram da suka yi saranda ga dakarun soji makon da ta gabata kuma suka mika makamansu.

Gwamnatin jihar Borno ta ce za ta sakar wa Ruth zabin yadda take son ta tafiyar da rayuwarta, kuma Gwamnati za ta tallafa mata wajen ganin ta sami ingattamcen rayuwa kamar kowa. Kuma za a taimaka mata wajen ganin an samar da tsarin da zai taimaka domin kawar da kyama, ko tsangwama a cikin al'umma domin ganin sauran yan matan Chibok da aka sace sun dawo lafiya kalau kamar yadda Ruth ta dawo.

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE