Dalilai guda 5 da ya sa kada ka yi gaggawa a rayuwarka


Abubuwa 5 da ya kamata ka kiyaye aikatawa a rayuwarka

1. Idan za ka gina, ko tsara kasuwancinka, kada ka yi gaggawa.

2. Kada ka yi gaggawa wajen yin aure. Ka natsu ka hankaltu kuma ka bi sharudda da ka'idodin addini da al'ada zamantakewar kafin ka yi aure.

3. Kada ka tsunduma cikin wata harkalla da zai bukaci kudade masu yawan gaske, ka yi bincike kuma ka raba kudin gida 2 ko 3 domin kaucewa zuba gaba dayan jarin ka a wuri daya idan harkar ta kwabe ya haifar da karayar arziki.

4. Kada ka yi gaggawa wajen yin alkawari. Domin kada ya zama Allah bai idar da nufinka ba ya kasance an sami matsala saboda alkawari da ka yi.

5. Kada ka dinga fallasa soyayyarka da wata a fili, domin kauce wa mugun ido da mugun gani har da mugun ji.

Allah kadai ne ya San daidai kuma shi kadai ne madogaran Dan Adam.

Source: isyaku.com

Martanin 'yan Najeriya ga IBB kan tsokacin rashawa da tayi katutu a gwamnatin Buhari

Cece-kuce ya barke tun bayan wani tattaunawa da aka yi da tsohon shugaban kasa na mulkin soji a ARISE TV inda yace mulkinsa ya yi yaki da cin hanci da rashawa fiye da mulkin shugaba Muhammadu Buhari.

Martanin 'yan Najeriya ga IBB kan tsokacin rashawa da tayi katutu a gwamnatin Buhari

IBB ya tunatar da yadda ya sauke gwamna akan satar N313,000 amma a halin yanzu mutane da dama da suka saci biliyoyin nairori suna yawonsu a cikin kasar nan

Wannan furucin nashi ya janyo cece-kuce, wasu suna sukar maganarsa yayin da wasu suka amince da maganarsa inda suke cewa rashawa tana kara yawaita a Najeriya.

Ga wasu daga cikin martanin jama'a

Daily Trust ta tattaro wasu daga cikin tsokacin jama'a. Misali daya daga cikin masu tsokaci ya zargi IBB da zama tushen rashawa a Najeriya.

A tarihi, IBB shine ya halasta rashawa a Najeriya,” a cewar wani Tunde Ayankoya a Twitter.

Wani Chris Ngonadi yace:

Tunda ba a rufeshi ba, mai zai hana yayi ta surutai. Ba laifin shi bane wannan shirmen da yake yi.

Amma duk da haka, akwai wadanda suke goyon bayan IBB inda suke cewa ta yuwu gaskiya ne.

A cewarsu baya ga rashawa, mulkin Buhari ta janyo ta’addanci mai yawan gaske.

Wani wanda yayi martani mai suna Danielmechi yace:

Babu ta’addanci a lokacin IBB, a lokacin mutanen kirki aka daura don su tafiyar da al’amuran kasa. Kuma cin hanci da rashawa bai yawaita ba.

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE