Da duminsa: Yan bindigan da suka sace Kwamishina a jihar Niger sun bukaci a basu N500m kafin su sake shi


Rahotanni daga jihar Niger sun ce yan bindigan da suka sace Muhammed Sanni Idris, sun nemi a biya su N500 kafin su sake shi. Shafin isyaku.com ya ruwaito.

Yan bindigan sun sace Kwamishinan ne a kauyensu da ke Baban Tunga a  karamar hukumar Tafa ranar Litinin 9 ga watan Agusta.

Bayanai sun ce tun safiyar Litinin ake ta ganawa kan lamarin karkashin jagorancin Mataimakin Gwamnan jihar Niger Ahmed Ketso.

Wata majiya ta gaya wa Daily Trust cewa yan bindigan sun tuntubi iyalinsa kuma sun bukaci a basu kudaden fansar har N500m.

Sai dai har yanzu  babu tabbacin bukatar da yan bindigan suka yi ga iyalin Kwamishinan daga  jami'an tsaro ko mahukunta a jihar Niger.

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN