Da duminsa: Yan bindiga sun sace wani shugaban jam'iyar APC a jihar arewa


Wasu Yan bindiga sun sace Mallam Aminu Bobi, wani tsohon shugaban jam'iyar All Progressives Congress (APC)  Zone ‘C’ a jihar Niger. Jaridar Legit ta ruwaito.

The Nation ta ruwaito cewa Yan bindigan sun sace Bobi ne ranar Asabar 7 ga watan Agusta da misalin karfe 5 na yamma lokacin da ya je duba wani aiki da ake yi a gonarsa da ke karamar hukumar Mariga a jihar Niger.

Wani ganau ya ce Yan bindigan su 18 kan babura 6 sun shiga gonar ne suka yi ta harbin mai uwa da wabi a iska kuma suka dauke shugaban na APC shi kadai suka bar sauran ma'aikatan da ke aiki a gonar.

A lokacin rubuta wannan rahotu, Kakakin hukumar yansandan jihar Niger DSP Abiodun Wasiu bai tabbatar da faruwar lamarin ba kafin yanzu. 

Previous Post Next Post