Da duminsa: An kashe sanannun yan bindiga sakamakon ragargazan da soji suka yi masu ta sama da kasa a Kaduna


Gwamnatin jihar Kaduna, ranar Lahadi tace sojoji sun kashe manyan sanannun yan bindiga huɗu a wata maɓoyarsu da aka fi sani da Maikwandaraso dake yankin karamar hukumar Igabi.


Dailytrust ta ruwaito cewa an kashe sanannun yan ta'addan ne a harin sama da dakarun sojin suka kai maɓoyarsu. Wannan na cikin harin haɗin guiwa da jami'an sojin ƙasa da na sama suka shirya kaiwaaɓiyar yan bindigan.

Kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida, Samuel Aruwan, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi. Ya jero sunayen yan bindigan da aka kashe waɗanda suka haɗa da Alili Bandiro, Dayyabu Bala, Bala Nagwarjo da Sulele Bala.

Yan Bindiga nawa sojojin suka kashe? Kwamishinan ya cigaba da cewa yan bindiga da yawan gaske sun hallaka a yayin harin ta sama da kuma ƙasa.

Wani sashin jawabin yace: "Yayin da gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i ya samu rahoton wannan nasara ya nuna jin daɗinsa da gamsuwarsa bisa namijin kokarin da sojoji ke yi na kawo karshen yan bindiga a maɓoyarsu."

Source: Legit Hausa

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE