Da duminsa: An kama wani mutum bayan ya yi wa matarsa saki uku nan take ta waya daga Saudiyya


Ƴan sanda a Saudiyya sun ce sun gurfanar da wani mutum bisa zarginsa yi wa matarsa saki uku nan take ta wayar salula. BBC Hausa ta ruwaito.

Ba a son yin saki uku nan take a shari’ar musulunci.

A cikin ƙorafin da ta gabatar, matar mai suna Razia Bano ta yi zargin cewa mijinta Tasabbul ya yi mata saki uku saboda iyayenta sun kasa biyan buƙatunsa na sadaki, kamar yadda ƴan sanda suka bayyana.

Ƴan sandan sun ce ƙarar ta shafi wasu dangin Tasabbul guda takwas.

Bano ƴar asalin ƙauyen Chak Auhadpur ta auri Tasabbul da ke yankin gundumar Mohammadpur Gaunti a ranar 21 ga watan Mayun 2005.

Ƴan sanda sun ce bayan auren, matar ta sha wahala a hannun Tasabbul da danginsa. Kuma a cewar jami’in ɗan sanda A K Gautam ya ce a ranar Litinin Tasabbul wanda ke aiki a Saudiyya yi wa matarsa saki uku ta wayar tarho.

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari