Da duminsa: An kama saurayi turmi tabarya yana lalata da saniya bayan ya tube sumbur


Wani mutum ya ba mazauna garin Kinyach da ke gundumar Baringo ta arewa mamaki a kasar Kenya bayan an kama shi turmi tabarya yana lalata da Saniya cikin duhun dare. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.

Wani abin mamaki shine yadda wanda aka kama mai suna Jackson Kakugo wanda ke cikin shekarunsa na 20, ya shiga shingen da makwabcinsa ke kiwon shanaye, ya je wajen wata Saniya ya tube zindir kafin ya fara lalata da ita. 

Sai dai bayan mai shanayen ya kama Jackson wanda da farko ya dauka barawo ne da ya je domin ya sace masa shanu, amma Jackson ya tabbatar masa lokacin da yake masa tambayoyi bayan ya kama shi cewa shi ya ketara zuwa cikin shingen shanu ne domin ya yi lalata da Saniya.

Sarkin garin Kinyach, Chief Eric Chebet ya tabbatar da faruwar lamarin. Sai dai Dattijan garin sun yi umarni a yi wa Jaxkson bulala daga bisani aka sake shi ya tafi.

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN