Da duminsa: Gurneti ya tashi da kananan yara 5 a Ngala, jihar Borno


Yara biyar sun halaka yayin da wani gurneti da suke wasa dashi ya fashe a garin Ngala dake jihar Borno, arewa maso gabas na Najeriya kusa da iyakar Kamaru, sojoji suka sanar da AFP a ranar Juma'a. Jaridar Legit ta ruwaito.

Yaran kanana uku sun tsinto abu mai fashewan yayin da suka je kiwo a wajen garin kuma ya tashi a hannunsu yayin da suke wasa da shi, cewa Umar Kachalla.

Biyu daga cikinsu sun mutu a take yayin da uku daga cikinsu suka rasu a wani asibiti dake Mada, cikin Kamaru, yace.

Mene ne tushen al'amarin?

Wani mayakin mai suna Umar Ari, ya bada makamancin labarin kan abinda ya faru a ranar Alhamis.

A watan Augustan 2014, mayakan Boko Haram sun kwace Ngala tare da wani birnin kasuwanci mai makwabtaka dasu mai suna Gamboru, Daily Trust ta ruwaito.

Dakarun sojin Najeriya sun kwace biranen biyu a watan Satumban 2015 tare da kokarin dakarun sojin Chadi bayan wata daya da suka kwashe suna yi wa miyagun aman wuta.

Ari ya ce har a yanzu ana samun gurneti daga ragowar wannan arangama tsakanin sojojin da miyagun, hakan yake kawo ajalin yara dake tsintosu.

Daily Trust ta ruwaito yadda a watan Disamban 2019, mutum tara sun halaka kuma 26 suka samu rauni sakamakon abu mai fashewa da ya tashi a gadar data hada Gamboru da Fotokol.

Mazauna yankin sun dora alhakin tashinsa da wani gurnetin da aka gani tamkar abun wasa wanda 'yan ta'addan Boko Haram suka baiwa yara a matsayin kyauta.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN