Da duminsa: An ceto ƙarin ɗaliban sakandaren Birnin Yawuri daga hannun 'yan fashi


Shafin BBC Hausa ya ruwaito cewa , Rundunar 'yan sandan Jihar Zamfara a Najeriya ta ce ita ce ta ceto ɗalibai biyu na sakandaren Birnin Yawuri ta JIhar Kebbi da 'yan bindiga suka sace a watan Yuni.

Tun farko dai rahotanni sun bayyana cewa mazauna garin Dandalla ne suka tsinci ɗaliban na Federal Governent College, Birnin Yauri suna watangaririya a dajin Dansadau na Ƙaramar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara ranar Asabar.

Sai dai da yake yi wa manema labarai jawabi a yau Lahadi, Kwamishinan 'Yan Sandan Zamfara Hussaini Abubakar ya ce jami'ansu ne suka yi nasarar ceto Maryam Abdulkarim mai shekara 15 da Faruk Buhari mai shekara 17.

"Ina mai shaida muku cewa a ranar 31 ga watan Yuli [Asabar], dakarun rundunar 'yan sanda ta musamman mai suna Operation Restore Peace suka yi nasarar ceto yaran," a in ji CP Hussaini.

Ya ce Maryam 'yar garin Wushishi ce da ke Jihar Neja, shi kuma Faruk ya fito ne daga Wara na Jihar Kebbi. An ceto su ne daga wani daji da ke ƙauyen Babbar Doka a garin Dansadau.

A ranar 17 ga watan Yuni ne 'yan bindiga suka kutsa makarantar sakandaren ta garin Yawuri suka sace ɗalibai fiye da 30 da wasu malamansu.

Rundunar sojan Najeriya ta ce ta ceto wasu daga cikin ɗaliban sannan ta kashe 'yan fashin kusan 80.

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN