Da dumi dumi: Wutar lantarki ya kashe barawo da ya hau cabe domin ya saci wayar wuta (Hotuna)


Wani mutum da ba a san ko waye ba kawo yanzu, ya mutu yayin da yake kokarin satar wayar wutar lantarki a hanyar tsohuwar Itu da ke Uruk Uso a garin Ikot Ekpene a jihar Akwa Ibom. Shafn labarai na isyaku.com ya tattaro.

 Ana zargin cewa wannan mutum ya mutu ne cikin daren ranar Talata 17 ga watan Agusta lokacin da jama'a ke barci.

Jama'a sun wayi gari kawai suka gan gawar makale a kan caben manyan wayoyin lantarki ranar Laraba da safe.

An kira jami'ai da suka zo suka saukar da gawar, sai dai har lokacin rubuta wannan rahoto, shafin isyaku.com ya gano cewa ba a gane gawar ko waye ba kawo yanzu.


Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari