Da Dumi-Dumi: Malamai da Dalibin Kwalejin Zamfara Sun tsero Daga Hannun Yan bindiga


Malamai biyu da ɗalibi ɗaya daga cikin waɗanda aka sace a kwalejin Noma dake Bakuri, jihar Zamfara sun tsero daga hannun yan bindiga, kamar yadda punch ta ruwaito.

Mataimakin shugaban kwalejin, Ali Atiku, shine ya bayyana haka ga manema labarai ranar Litinin.

Atiku Yace:

"Biyu daga cikin malamai da kuma ɗalibi ɗaya sun tsero daga hannun yan bindiga bayan sun sace su, sun komo makaranta da safiyar Litinin.

"Zuwa yanzun da nake magana da ku mun gano cewa maharan sun sace ɗalibai 15 duk maza, sai kuma malamai nata uku da namiji ɗaya, kuma sun kashe jami'an tsaron mu guda biyu."

Me hukumar yan sanda tace game da lamarin?

Har zuwa yanzun da muke kawo muku wannan rahoton hukumar yan sanda reshen jihar Zamfara ba tace uffan ba game da lamarin.

A baya, yan bindiga sun taba sace shugaban kwalejin aikin noma dake Bakura, Alhaji Habibu Mainasara

Sai dai daga baya ɓarayin da suka yo garkuwan da shi sun sako shi bayan an biyasu kuɗin fansa

Source: Legit

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari