CJN Tanko ya yi kiran gaggawa ga manyan alkalan jihar River, Kebbi, Cross River, Anambra, Jigawa da Imo kan hukuncin da suka zartar a rikicin PDP


Shugaban alkalan Najeriya (CJN), Justice Tanko Muhammad ya tattaro manyan alkalan jihar River, Kebbi, Cross River, Anambra, Jigawa da Imo don taron gaggawa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan ya biyo bayan hukuci mabanbanta da ko wannensu ya yanke a jiharsa masu karo da juna.

A makon da ya gabata ne kotu biyu suka yanke hukunce-hukunce masu karo da juna dangane da rikicin da ya barko jam’iyyar PDP.

Yayin da babbar kotun jihar Rivers ta dakatar da Uche Secondus daga zama shugaban jam’iyyar na kasa, sai kuma kotun jihar Kotu ta dawo da shi.

Sannan akwai hukunce-hukuncen da suka danganci wasu jam’iyoyin wadanda suka kawo rikici, Daily Trust ta ruwaito hakan.

A takardar gayyatar ta ranar 30 ga watan Augustan 2021 da shugaban alkalan ya aika don gayyatar alkalan, ya na bukatar su bayyana a gaban sa don zaunawa a kan wadannan hukunce-hukuncen.

Rahotun Jaridar Legit

An janyo hankalina a kan illolin da hukunce-hukuncen da wasu kotu suka yanke wanda ko wanne ya ci karo da wani.

Don haka ya zama tilas a kaina in gayyace ku don mu zauna mu tattauna a kan wannan lamarin. Wannan ya ci karo da yadda NJC ya hana yanke hukunci mabanbanta musamman dangane da matsalolin cikin jam’iyya.

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari