Bayan ficewar sojin Amurka, Yan Taliban sun kama babban birnin na biyu a Afghanistan


Kungiyar Taliban a Afghanistan ta ce ta kwace birnin Sheberghan da ke arewacin kasar, wanda idan har hakan ta tabbata to birnin zai kasance babban birnin lardi da ya fada hannun kungiyar a cikin kwanakin nan bayan Zaranj da ke kudu maso yammaci da ya shiga hannunta ranar Juma'a.

Sai dai mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Afghanistan ya ce har yanzu dakarun gwamnati na cikin birnin na Sheberghan, kuma nan da dan lokaci za su yi waje da mayakan na Taliban.

Sheberghan, wanda shi ne babban birnin lardin Jawzjan, nan ne babbar tungar mayakan tsohon mataimakin shugaban kasar ta Afghanistan Abdul Rashid Dostam.

Sakamakon hare-haren na 'yan Taliban an ce dakarunsa wadanda ke yakar 'yan Taliban a wannan bangare sun ja baya zuwa yankin filin jirgin saman birnin.

Yayin da su kuma 'yan Taliban suka ce sun kama gidan yarin birnin sun kuma saki daruruwan 'yan kaso da ke tsare.

Kungiyar ta kuma rufe wata muhimmiyar hanya ta tsallaka iyakar kasar da Afghanistan a ranar Juma'a, a matsayin martani na tsananta ka'idojin bayar da izinin shiga ga 'yan kasar ta Afghanistan, matakin da ya bar daruruwan matafiya curko-curko, ba su da ta yi.

A garin Chaman da ke bangaren kasar Pakistan a kan iyakar mutane da dama sun shaida wa BBC cewa lamarin ya rutsa da su, sun kasa komawa gida.

A da dai babu wani bayani da aka samu dangane da harin daga gwamnatin kasar, amma daga bisani kakakin ma'aikatar tsaron kasar ya gaya wa BBC cewa har yanzu dakarun gwamnati na cikin birnin kuma za su kawar da mayakan na Taliban ba da jimawa ba. In ji shi.

Idan dai har dakarun gwamnatin ba su yi nasarar fatattakar 'yan Taliban daga birnin ba, to wannan zai kasance, koma-baya na baya- bayan nan ga gwamnati, kwana daya bayan da 'yan tawayen suka kama Zaranj, babban birnin lardin Nimroz.

Jami'an gwamnatin Afghanisatn sun ce can ma a biranen Lashkar Gah da ke kudu da kuma Kunduz da ke arewa ana mummunan ba-ta-kashi. Kuma rahotanni na cewa an kashe farar hula da yawa a Kunduz.

A Kabul ma babban birnin kasar Taliban ta ce ta kai wani harin bam, har ta kashe wani matukin jirgin yakin gwamnati. Kungiyar masu tayar da kayar bayan ta takura dakarun gwamnatin kasar, ta hanyar kai hare-hare a lokaci guda a manyan birane a 'yan makonnin nan.

Kuma kungiyar ta kama gomman gundumomi tun bayan da dakarun hadaka na kasashen suka fara ficewa daga kasar wata uku da ya gabata.

Kazamin yakin ya tilasta wa mutane sama da dubu dari uku da hamsin tserewa daga gidajensu. Gommai kuma sun mutu zuwa yanzu.

Sakamakon kazantar lamarin gwamnatocin Amurka da Birtaniya sun bukaci 'yan kasashensu da su bar kasar ba tare da bata wani lokaci ba.

Rahotun BBC Hausa

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN