Ban ki yin biyayya ga umarnin Osinbajo ba, Abubakar Malami - ISYAKU.COMAntoni janar na tarayya kuma ministan shari'a, Abubakar Malami SAN, ya musanta rahotanni dake yawo na cewa ya bijirewa umarnin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a kan zabukan jam'iyyar APC. Jaridar Legit ta ruwaito.

Daga cikin umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Farfesa Osinbajo yayi taron manyan lauyoyi na jam'iyyar a ranar 30 ga watan Yuli domin shawo kan matsalar dake cikin jam'iyyar bayan kotun koli ta yanke hukunci kan zaben gwamnoni na jihar Ondo.

Ban ki yin biyayya ga umarnin Osinbajo ba, Abubakar Malami

Ban ki yin biyayya ga umarnin Osinbajo ba, Abubakar Malami. Hoto daga Channelstv.com

An zargi Malami da bijirewa Osinbajo

Akwai rahotanni dake yawo na cewa Osinbjo ya umarci Malami da kada a yi zabukan jam'iyyar na jihohi, Daily Trust ta wallafa.

Tun farko Malami ya sanar da Daily Trust cewa bai bijirewa umarnin fadar shugaban kasan ba. Ya ce ya bada shawara a yi zabukan ne a matsayinsa na lauya ba na antoni janar na shari'a ba.

A wata takarda da mataimakin Malami na musamman a harkar yada labarai, Umar Gwandu ya saka hannu, AGF yace yadda za a tsara zabukan jam'iyyar abu ne da ya shafi jam'iyyar APC kuma bashi da alaka da na ministan.

Malami ya musanta zargin da aka yi masa

Akwai matukar amfani idan aka bayyana cewa zabuka tare da tarukan jam'iyya duk alhaki ne na jam'iyyar siyasa ba na ofishin antoni janar ba.

Mai girma antoni janar na tarayya da ministan shari'a ba shine ke da alhakin tabbatar da an bi umarnin da ya shafi shugabancin jam'iyya ba kamar yadda aka sani.

A don haka, bai dace da hankali ba idan ake cewa mai girma antoni janar ya ki bin doka wacce bashi da ikon sakawa a shari'ance.

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE