An kashe babban dan Sanatan jihar Kebbi Bala Ibn Na'Allah


Wasu da ba a san ko su waye ba kawo yanzu sun kashe babban Dan Sanata Bala Ibn Na:Allah dan shekara 36 mai suna Abdulkarim Bala Ibn Na'Allah. An Sami gawarsa a gidansa da ke unguwar titin Umar Gwandu da ke Malali a Kaduna. Shafin labarai na isyaku.com ya wallafa.

Rahotanni sun ce da tsakar ranar Lahadi da karfe 12 na rana,  29 ga watan Agusta, wasu mutane suka shiga gidansa suka daure shi a dakinsa sakamakon haka ya mutu, daga bisani suka kwashe wasu kayakinsa da motarsa suka gudu.

Daily Trust ta labarta cewa mutanen sun shiga gidan ne bayan sun haura ta bayan gidan suka kware kwano kuma suka shiga gidan ta silin.

Kafin mutuwarsa, Abdulkarim matukin Jirgin sama ne.

Mahaifinsa Sanata Bala Ibn Na'Allah shi ne Sanata mai wakiltar Kudancin jihar Kebbi a zauren Majalisar Dattawan Najeriya.Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari