An kama wani kato da ke shiga irin ta mata, duba abin da ya faru (Hotuna)


Yan banga a karamar hukumar Adayi a jihar Kogi sun damke wani katon da ya yi shiga irin ta mata.

An cafke mutumin mai suna Ilyasu ranar Laraba 25 ga watan Agusta a unguwar Zariagi a karamar hukumar Adavi bayan take takensa ya haifar da shakku a unguwar.  An kama shi sanye da dan guntun buje da gashin kai irin na mata.

Shugaban karamar hukumar Adayi Hon. Joseph Omuya Salami, ya je wajen da lamarin ya faru nan take, kuma ya ba yan bangan umarnin cewa su mika wanda aka kama ga jami'an soji da ke unguwar domin gudanar da bincike.

Sai dai wanda aka kama ya tabbatar da cewa sunansa Iliyasu, dan asalin karamar hukumar Ofu ne a jihar Kogi, ya ce shi mai sana'ar yin rawa ne. Ammaan kasa samun wanda ya san shi a cikin al'ummar garin balle a tabbatar da hakikanin gaskiyar ikirarinsa.
 

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari