An kama kifi mai irin hakoran dan adam cike a bakinsa (Hotuna)


An kama wani kifi mai hakora kamar na dan adam a kasar Amurka, lamari da ya ba jama'a masu zuwa bakin Teku domin shakatawa mamaki.

Shafin isyaku.com ya samo cewa wani mai kamun kifi, mai suna Jennette's Piere ne ya kama shi a shahararren wajen kamun kifi na Nag's Head, a Arewacin Carolina.


Bayan hotunan kifin sun zagaya shafukan intanet, an samo cewa kifin na cikin jinsin kifi da ake kira sheepshead fish.


Wanda ya kama kifin ya ce yana sha'awar kamun kifi, amma da farko ya tsorata bayan ya yi ido biyu da kifi wanda bakinsa ke cike da hakora masu kama da na dan adam.

Jerin sunaye: Kaduna, Jigawa, Kebbi da wasu jihohi 10 sun samu sabbin kwamishanonin yan sanda

Sifeto Janar na yan sanda, Usman Baba Alkali, ya bada umurnin nada sabbin kwamishanonin yan sanda na jihohi 13, da birnin tarayya Abuja.

Kakakin hukumar, Frank Mba, a jawabin da ya saki ta shafin hukumar ta Facebook ranar Juma'a, 6 ga agusta, ya yi bayanin cewa an yi wannan sauyi ne domin kawo inganci ga tsaro.

Frank Mba yace jihohin da aka nada sabbin kwamishanoni sune:

1. Jihar Niger , CP Monday Bala Kuryas
2. Jihar Kwara, CP Emienbo Tuesday Assayamo
3. Jihar Nasarawa, CP Soyemi Musbau Adesina
4. Jihar Taraba , CP Abimbola Shokoya
5. Jihar Benue, CP Akingbola Olatunji
6. FCT Abuja, CP Babaji Sunday
7. Jihar Kogi, CP Arungwa Nwazue Udo
8. Jihar Kaduna, CP Abdullahi Mudashiru
9. Jihar Jigawa, CP Aliyu Sale Tafida
10. Jihar Enugu, CP Abubakar Lawal
11. Jihar Cross River, CP Alhassan Aminu
12. Jihar Bayelsa, CP Echeng Eworo Echeng
13. Jihar Kebbi, CP Musa Baba

Kakakin yan sandan ya ce sauran manyan jami'an yan sandan da aka sauya da wurin aiki sune:
CP Ndatsu Aliyu Mohammed, a tsohon kwamishanan Enugu wanda aka mayar yanzu kwamishanan sashen yaki da damfara FCID, Abuja CP Sikiru Akande, tsohon kwamishanan Cross River wanda yanzu aka mayar dashi sashen ICT a hedkwata Abuja. CP Bankole Lanre Sikiru: CP INTERPOL, FCID Lagos; CP Augustine Arop mataimakin kwamandan makarantar yan sanda dake Jos.

Source: Legit

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN