An kama katti 3 da suka sace wata mata suka nemi a basu N500m, duba yadda ta faru


An cafke wasu mutane uku bayan sun sace wata mata suka nemi kudin fansa a yankin Ogombo/Lekki Ajah a jihar Lagos.

Jami'an yansanda sashen Intelligence Response Team na ofishin yansanda da ke Ogombo a jihar Lagos ne suka kama mutanen bayan sun bukaci a biya su N500m kafin su saki matar da suka kama.

CSP Adekunle Ajisebutu, shi ne Kakakin hukumar yansandan jihar Lagos, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce an kuɓutar da wacce aka kma kuma ta koma cikin iyalinta.

Ya ce an mika masu garkuwan zuwa sashen binciken kwakwaf na CID domin ci gaba da bincike.

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN