An kama ƙasurgumin dan fashi da makami a Kano bayan mahaifinsa ya kore shi daga gidansa, duba abin da ya faru (Bidiyo)


Jami'an yansandan jihar Kano sun kama wani matashi dan shekara 26 mai suna Mohammed Ibrahim bayan ya aikata fashi da makami. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.

Kakakin hukumar yansandan jihar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar wa manema labarai.

Ya ce an kama.dan fashin ne ranar 16 ga watan Agusta bayan ya aikata fashi da makami. Ya ce wanda aka kama ya gaya wa yansanda cewa ya sha aikata laifin fashi da makami.

Ya ce an taba daure shi a Kurkuku tsawon watanni uku ba tara bayan ya aikata laifin sata.

Ya ce Yana da budurwa (Karuwa) a Unguwar Sabon gari Kano inda yake rayuwa da ita bayan mahaifinsa ya kore dhi daga gida sakamakon aikata laifin sace sace da mallakar bindiga.

Kalli bidiyon cikakken bayani:

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN