An dakatar da Abba Kyari daga aikin dansanda


Shafin BBC Hausa ya ruwaito cewa Rundunar 'yan sandan Najeriya ta dakatar da Abba Kyari daga aikin ɗan sanda sakamakon zargin karɓar cin hanci da 'yan sandan Amurka ke yi masa.

Hukumar Kula da Harkokin 'Yan Sanda ta ɗauki matakin dakatar da Mataimakin Kwamishinan 'Yan Sanda DCP Kyari ne biyo bayan shawarar da Sufeto Janar na 'Yan Sanda Usman Alkali Baba ya bayar.

Mai magana da yawun hukumar, Ikechukwu Ani, ya faɗa cikin wata sanarwa cewa dakatarwar za ta fara aiki ne daga ranar Asabar 31 ga watan Yuli.

"Matakin zai ci gaba da aiki har zuwa lokacin da za a kammala binciken zargin da Federal Bureau of Investigation [FBI] ke yi masa," a cewar sanarwar.

IGP Usman Alkali ya kafa kwamati na mutum huɗu ƙarƙashin jagorancin DIG Joseph Egbunike wanda zai binciki zargin da ake yi wa Abba Kyari, wanda shi ne shugaban tawagar tattara bayanan sirri ta Police Intelligence Response Team (IRT).

Ana zargin Abba Kyari da karɓar cinhanci a hannun matashi ɗan Najeriya kuma mazaunin Amurka mai suna Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppy, domin kamawa da kuma muzguna wa wani abokin harkarsa, Kelly Vicente. Sai dai Kyari ya musanta zargin.

Hushpuppy ya bayyana cewa ya bai wa Mista Kyari rashawar ce yayin da hukumar tsaron FBI ta Amurka ta kama shi bisa zargin aikata damfara da zamba a kan kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane.

Sai dai rundunar ta ce har yanzu tana ɗaukar Abba Kyari a matsayin maras laifi har sai bincike ya tabbatar da laifin nasa.

Zargin da ake yi wa Abba Kyari

Abba Kyari

ASALIN HOTON,FACEBOOK/ABBA KYARI

Jami'in ɗan sanda Najeriya, Abba Kyari ya musanta karba rashawa a hannun Raymond 'Hushpuppi' Abbas.

Sashen shari'a na Amurka ya ce ya kama wasu ƴan Najeriya mazauna Amurka uku da suka taimaka wa Raymond 'Hushpuppi' Abbas ya yi damfarar dalar Amurka miliyan 1.1.

Cikin wata sanarwa wadda sashen ya fitar a ranar 28 ga watan Yuli, ta ce Hushpuppi ya amsa laifin halasta kudaden haram da wasu laifukan masu alaka da kasuwancin intanet.

Kuma sun yi zargin cewa Hushpuppi ya bai wa mataimakin kwamishinan ƴan sandan Najeriya Abba Kyari cin hanci domin kama takwaransa Kelly Vicente mai shekara 40 da haihuwa.

Bayanin sahsen shari'ar ya bayyana hakan ne bayan da Vicent ya yi kokarin tona asiri da kuma ba da bayanai kan zargin abin da suka yi masa.

"A cewar sanarwar, Abba kyari wanda babban mataimakin shugaban 'yan sandan Najeriya ne, shi ake zargi da kitsa kama Vicent tare da aike wa da shi gidan yari, ya kuma dauki hotonsa ya aika wa Abbas.

"Abba Kyari kuma an yi zargin ya aika wa Abbas bayanin asusunsa na banki wanda nan ne Abbas ya aika masa kuɗaɗen ladan kama Vicent tare da tusa keyarsa gidan yari,"kamar yadda bayanin kotun ya bayyana.

Amma Abba Kyari ya musanta zargin yana cewa bai karbi ko sisi ba daga Hushpuppi.

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN