Yanzu yanzu: Kotu ta hukunta mahaifin da ya daure dansa a turakun dabbobi a unguwar Badariya a garin Birnin kebbi, duba hukunci


Babbar Kotun Majistare da ke zamanta a garin Birnin kebbi ta daure Aliyu Umar tsawon shekara daya a gidan gyara hali bayan ta kama shi da laifin cin zarafin dan shi ta hanyar daure shi a turakun dabbobi har tsawon shekara daya a Unguwar Badariya da ke garin Birnin kebbi.

Alkalin Kotun ya yi la'akari da cewa

1. Mahaifin yaron ya ci zarafinsa ta hanyar daure shi a turakun dabbobi

2. Kotu ta aminta cewa yaron ya shiga matsanancin hala'in kuncin rayuwa sakamakon daurin da aka yi masa tare da dabbobi. Sakamakon radadin balin da hakan ya haifar ga rayuwarsa ya kai matsayin yana tsintar bahayan dabbobi yana ci.

3. Kotu ta gamsu cewa da gangan mahaifin yaron ya daure shi ba tare da shawara ko izinin Likita ko kwararru ba.

4. Mahaifin yaron ya yi ikirarin a rubuce ga yansanda masu bincike, cikin natsuwa cewa ya daure yaron tare da dabbobi.

5. Kotu ta ki ta amince da bukatar jaye kalmar cewa mahaifin yaron ya "DAURE" shi, bisa la'akari da shaida ta "A" da "B" inda shi mahaifin yaron da kanshi ya yi bayani a rubuce cewa lallai ya daure yaron, har ya bayar da hujjojin da ya sa ya yi haka. Kotu ta karanto ayoyin doka na dalilin da ya sa ta ki amincewa da yunkurin Jaye kalamansa.

6. Kotu ta ki amincewa da dalilin da mahaifin yaron ya bayar cewa yaron yana da tabin hankali kuma yana jifan motocin jama'a da jawo rigima, kuma ya daure shi ne saboda kada ya raunata kansa.

Kotu ta ce bai kamata mahaifin yaron ya daure shi ba alhalin yana da zabin da zai kai yaron Asibitin mahaukata domin samun wadataccen kulawa daga Likitan mahaukata. Ya ce babu wata shawara ko izini daga kwararru bisa wannan dalili da sauran dalilai Kotu ta yanke wa mahaifin yaron hukunci.

HUKUNCI

Bayan Alƙali Mungadi ya binciko tanadin hukunci da doka ta tanada kan wanda aka kama da laifin cin zarafin dansa a Dokokin Penal Code na jihar Kebbi.

Alkalin Kotun ya karanto wa Aliyu Umar hukunci da doka ta tanada. Ya ce sashe na 238 na Penal Code ya tanafi daurin shekara biyar ko tara, ko duka biyu ga duk wanda aka kama da laifin cin zarafin dansa a jihar Kebbi.

Sai dai kafin ya idar da zartar da hukunci  Lauyan mahaifin yaron ya mike ya nemi afarmar Kotu, cewa ta tausaya wa mahaifin yaron kuma ta yi masa sassauci a hukunci, tunda wannan ne karo na farko da ya aikata irin wannan laifi.

Alkalin Kotun ya daure Aliyu Umar tsawon shekara daya a gidan gyara hali ba tare da zabin biyan tara ba. 

Alkalin Kotun ya ce ya zana wajibi Kotu ta yi adalci wajen yanke hukunci a wannan sharia domin ya zama izna ga wadanda ke aikata, ko suke da niyyar aikata irin wannan laifi nan gaba. Ya ce mahaifin yaron zai iya daukaka kara cikin kwana 30 daga yau idan har bai gamsu da hukuncin Kotu ba.

Wannan ya kawo karshen wannan shari'a da aka shafe wata takwas (8) ana yi, kuma ya zo karshe ranar Alhamis 29 ga watan Yuli 2021 da karfe 3:30 na rana.

INA MAKOMAR IYALINSA ?

Aliyu Umar dattijo ne mai shekara 67 a Duniya, wanda ke da matan aure guda uku da yaya goma sha takwas (18). Kuliya manta sabo yau ta raba jagoran gida da matansa tare da yaransa sakamakon kuskure kan yaro daya daga cikin gida da ke da mutum 22. Za a tsare mutum daya kuma jagoran gida wanda shi ke dauke da dawainiyar gidansa tare da jama'a da ke ciki.

Allah ka kare mu daga kaddarorin rayuwa, ka sa mu gama lafiya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN