Yanzu yanzu: Allah ya yi wa mahaifiyar Ibrahim Abdulazeez na muryar Amurka rasuwa


Allah ya yi wa mahaifiyar marigayi Ibrahim Abdulazeez Wakilin Muryar Amurka mai suna Hajiya Biba rasuwa. An fi saninta da suna Mamman.

Ta rasu a garin Mayo Belwa da safiyar Asabar 3 ga watan Yuli, 2021. 

Za a yi jana'izarta a garin Mayo Belwa na jihar Adamawa.


Marigayi Ibrahim Abdulazeez, shahararren Dan Jarida ne Wanda ya wakilci gidan rediyon Muryar Amurka a jihohin Adamawa, Bauchi da Gombe, ya rasu cikin watan Fabrairu na wannan shekarar, wata biyar tsakanin rasuwarsa da rasuwar mahaifiyarsa ranar Asabar.

Amadadin dukkan ma'aikatan shafin labarai na ISYAKU.COM, Malam Isyaku Garba Zuru, Mawallafin shafin, yana isar da ta'aziyyarsu ga iyalai, yan'uwa da abokan arziki ga marigayi Ibrahim. Tare da fatar Allah ya gafarta masa tare da mahaifiyarsa ya amshi bakoncinsu kuma ya hore masu Aljannah. Ya sa mu cika da Imani tare da yin kyakkyawan karshe. Amin. 

Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari