Yadda wasikar Jakadan Najeriya, Tukur Buratai ta taimaka wajen cafke Igboho a kasar Benin


Tsohon shugaban hafsun sojojin kasa na Najeriya, Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya), ya taimaka wajen cafke Sunday Igboho a Benin.

Crime Channels ta ce Tukur Yusuf Buratai ya bada gudumuwa wajen kama wannan mutumi tare da mai dakinsa, Rapo, a hanyarsu ta zuwa kasar Jamus.

An dade da gane gudun ruwan Igboho

Rahotanni sun bayyana cewa hukumomi da jami’an Najeriya sun dade da gano inda Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya boye.

Jami’an tsaro sun kyale Sunday Igboho ne domin su iya kama shi cikin ruwan sanyi, ba tare da an zubar da jini ba, hakan kuwa aka yi a daren Talatar nan.

A lokacin da Igboho ya samu takardar fasfon bogi, sai gwamnatin tarayya ta kara sa masa ido.

Najeriya ta sanar da kasashen da ta ke makwabtaka da su cewa su yi hattara da Igboho. A ranar Litinin aka kama shi a filin jirgin Cadjèhoun da ke Cotonou.

Takardar Buratai ta hana Igboho zuwa Jamus

Tukur Yusuf Buratai wanda bai dade da zama Jakadan Najeriya a kasar Benin ba, ya rubuta wa gwamnatin kasar Benin takarda a game da wannan mutum.

Buratai ya na aiki ne tare da jami’an tsaron leken asiri na DSS da na harkokin kasashen waje, NIA.

Wani jami’in tsaro ya sanar da PRNigeria cewa Janar Buratai (mai ritaya), ya dage a kan sai an kama Igboho, kuma an dawo da shi Najeriya daga Cotonou.

Takardar sabon jakadan ya shiga hannun gwamnatin Benin ne ta ofishin jakadancin Najeriya, wannan ya taimaka sosai wajen hana shi zuwa kasar Jamus.

Lauyan Sunday Igboho, Yomi Alliyu SAN ya ce Igboho da mai dakinsa, su na kokarin hawa jirgin sama zuwa kasar Jamus ne sai jami'an Interpol suka cafke su.

Alliyu ya ce bai kamata a dawo da Igboho gida ba,kamar yadda yarjejeniyar dake tsakanin gwamnatin Najeriya da sauran kasashen Afirka ta tanada.

Source: Legit

 • 0/Post a Comment/Comments

  Rubuta ra ayin ka

  Previous Post Next Post

  Reported by ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
  https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
  LATSA NAN 

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

  Facebook.com/isyakulabari