Yadda maciji ya sari tsoho mai shekara 65 a al'aurarsa lokacin bahaya a bandaki


Maciji ya sari wani tsoho mai shekara 65 a al'aura da sanyin safiyar a lokacin da ya zauna domin yin bahaya a bandaki a kasar  Austria.

Da misalin karfe shida na safe ne lamarin ya faru lokacin da tsohon ya ke amfani da ban daki, sai ya ji cizon wani abu a al'aurarsa. Amma ko da ya duba sai ya gan maciji mai tsawon kafa 5 a cikin tukunyar bahaya da ke bandaki.

Nau'in majijin da ake kira reticulated python, nau'in macizai mesa ne da aka saba gani a Nahiyar Asia kuma za ta iya yin tsawo har zuwa kafa 30, watau mita 9.

An garzaya zuwa asibiti da tsoho domin samun kulawan Likita. An kira mai kama macizai ya tafi da macijin ya wanke bahaya da tsoho ya yi a jikinsa, kuma aka kai macijin wajen wanda ya mallake shi.

Daga bisani yansanda sun yi karar mai macijn wanda ya mallaki macizai 11 bisa zargin yin sakaci har macijinsa ya sari makwabcinsa .

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN