Yadda Jama'ar gari suka kwace masu garkuwa da mutane daga hannun yan banga suka aika su lahira nan take


Fusatattunm matasa sun kashe mutum biyar bisa zargin sace mutane domin karban kudin fansa a hanyar Afuze-Uokha da ke karamar hukumar Owan ta yamma a jihar Edo a cikin karshen mako.

Bayanai sun ce wadanda aka kama sun sace wasu matafiya ne a kan hanya, bayan sun farmake su rike da muggan makamai kuma suka tasa keyarsun zuwa cikin daji inda suke neman yanuwan mutanen cewa su kawo kudin fansa kafin su sako yanuwansu da suka sace.

Sai dai bayan yan Banga sun sami labari, sun yi  gangami kuma suka bi sawun wadannan masu garkuwa suka kama su a cikin daji.

Fusatattun jama'a da suka dade suna jin takaicin irin yadda batagari suka addabe su da sace sacen mutane da kwace kayakin mutane a yankin sun yi kukan kura suka kwace masu garkuwan daga hannun yan Banga da ke kan hanyarsu ta kai masu garkuwan wajen yansanda, suka kashe su kuma suka banka wa gawakinsu wuta.

Kakakin hukumar yansandan jihar Edo Kontongs Bello, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin amsa tambayoti daga manema labarai. Ya ce yansanda na ci gaba da gudanar da bincike.


 • 0/Post a Comment/Comments

  Rubuta ra ayin ka

  Previous Post Next Post

  Reported by ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
  https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
  LATSA NAN 

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

  Facebook.com/isyakulabari