Yadda jama'a suka taimaki matukin jirgin da 'yan bindiga suka harbo a Zamfara


Wasu mazauna yankuna a jihar Zamfara a ranar Litinin sun bada labarin yadda suka ceci matukin jirgin yaki jim kadan bayan ya sauka daga kumbo bayan hatsarin jirgin yakin a ranar Lahadi.

Har yanzu dai ba a san halin da sauran wadanda ke cikin jirgin suke ba, Daily Trust ta ruwaito.

Majiyoyi masu karfi sun sanar da Daily Trust cewa jirgin yakin ya fadi ne a wani yanki dake da kusancin kilomita 15 daga garin Dansadau.

Jirgin NAF: Yadda jama'a suka taimaki matukin jirgin da 'yan bindiga suka harbo a Zamfara

Wani mazaunin yankin ya ce: "Matukin jirgin saman ya sauka daga kumbo inda da gaggawa ya shiga yankin kusa. Bayan mutane sun gane abinda ya faru, sai suka yanke hukuncin boye shi ta yadda koda 'yan bindigan sun biyo shi ba zasu gan shi ba.

"An ga 'yan bindigan suna ta kaiwa da kawowa a inda jirgin saman ya fadi, ta yuwu neman wanda ya tsira suke yi."

Mazaunin yankin wadanda suka bukaci a boye sunansu sun ce: "Mauzauna yankin sun jira har faduwar rana sannan suka baiwa matukin jrigin kaya irin na kauyawa inda yayi basaja sannan suka fitar dashi zuwa garin Dansadau inda aka mika shi wurin hakimi."

"Da safe sai jiragen NAF biyu tare da na yaki daya suka iso domin ceton matukin jirgin. Jirgin ya sauka kusa da wata makarantar sakandare dake garin yayin da jirgin yakin ke ta kaiwa da kawowa. An mika musu matukin jirgin saman inda suka tafi da shi a take," wani ya sanar.

Akwai rahotannin dake yawo na cewa jirgin sojojin saman Najeriya wanda ya taso daga jihar Adamawa ya fadi a wani wuri a cikin jihar Kaduna.

Amma kuma yayin da aka tuntubi mai magana da yawun NAF, Edward Gabkwet, ya sanar da TheCable cewa babu wani hatsari da ya auku a Kaduna kamar yadda ya sanar da manema labarai.

Source: Legit

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN