Yadda Gwamnan Kaduna, Malam El-Rufa'i Ya Cire Ɗansa Daga Makarantar Gwamnati a Sirrince


Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ya cire ɗansa daga makarantar gwamnati a sirrin ce, kamar yadda daily trust ta ruwaito.

Yayin da gwamnan ya sanya ɗansa, Al-Sadiq, a makarantar gwamnati a bayyane, mutane da dama sun yi tsokaci a kan matakin gwamnan, amma cire shi da ka yi a sirrin ce yasa wasu ke ganin wannan yaudara ce da kuma rashin ingancin makarantun.

Babu wani ƙwakkwaran dalili da yasa gwamnan ya cire ɗansa, amma wasu masu tsokaci sun bayyana cewa saboda yawaitar satar mutane a makarantu ne yasa gwamnan ɗaukar wannan matakin.

Wasu kuma na ganin iyalansa ne suka matsa sai ya cire ɗan nashi ko kuma makarantun gwamnatin ne ba su da inganci.

Mazauna yankin da makarantar take, sun nuna rashin jin daɗinsu bisa matakin gwamnan na zare ɗansa bayan ya fara karatunsa tare da yaran talakawa.

A baya mutane da dama na ganin sanya ɗan El-Rufa'i a makarantar gwamnati wata dama ce da zaisa a gyara makarantun.

Mutanen Kaduna sun nuna rashin jin daɗinsu

Mazauna jihar Kaduna musamman waɗanda ke zaune a yankin makarantar da aka sanya El-Sadiq, sun bayyana damuwarsu kan matakin cire yaron.

Wani mai suna, Ibrahim Yero, yace:

"Bamu ji daɗin cire shi ba, saboda hakan ya nuna cewa saka yaron da aka yi a baya duk yaudara ce kawai."

"Ya kamata shugabanni sun rinƙa cika maganganunsu da alƙawurran su, bayan gwamna ya cire ɗansa daga makaranyar, yanzun kuma ya koma yana ƙara yawan kuɗin makaranta da korar malamai."

"Na kasa fahimtar inda gwamnan ya sa gaba, wani ya taimaka ya masa magana hakanan dan Allah."

Har yanzun gwamnatin jihar Kaduna ba ta yi martani kan lamarin cire ɗan gwamna El-Rufa'i ba.

Ranar da aka sanya yaron a makaranta

Lokacin da gwamna El-Rufa'i tare da matarsa, Ummi, suka saka ɗan su mai shekara 6 a makarantar gwamnati a 2019, yan Najeriya da dama sun yaba wa gwamnan.

Mutane da dama sun jinjinawa gwamnan tare da fatan cewa Malam El-Rufa'i ya ɗakko hanyar gyara ilimi a jihar Kaduna.

A wancan lokaci, wannan matakin gwamnan ya ƙara wa iyaye da dama ƙwarin guiwa cewa makarantun gwamnati suna da kyau, kuma yayansu zasu iya samun ilimi mai inganci.

Majalisar wakilan tarayya ta yi watsi da buƙatar ɗage dokar gwamnatin tarayya ta hana amfani da twitter, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Majalisar ta ɗauki wannan matakin ne yayin da take nazari kan rahoton kwamitocinta da suka gudanar da bincike.

Source: Legit

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN