Yadda aka aika dan fashi da ya addabi masu POS barzahu da gaggawa, duba wadanda suka aikata mashi


Jami'an rundunar yansandan jihar Imo sun bindige wani ƙasurgumin dan fashi da makami da ya addabi masu sana'ar POS a garin Egbu da ke karamar hukumar Owerri ta arewa ranar 21 ga watan Yuli.

CSP Michael Abattan, Kakakin hukumar yansandan jihar Imo ya ce Yan fashin sun buda wa yansanda wuta da bindigoginsu yayin da yansanda suka isa wajen da suke aikata fashi da makami.

Sakamakon haka yansanda suka mayar da martani nan take kuma suka bindige d


an fashi guda daya daga cikin sauran Yan fashin da ke tserewa kan manyan baburarn su da raunukan bindiga.

Yansanda sun kama babur na Dan fashin mai lamba IMO, AFR 387 OJ , da bindigar hannu kirar gida tare da harsashi cartridge guda 7. Yansandan sashen tactical team sun dukufa wajen ganin sun kama Yan fashin da suka tsere da raunukan harsashi a jikinsi.

Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari