Tsoho mai shekaru 90 ya shiga hannun NDLEA kan safarar miyagun kwayoyi


Wani tsoho mai shekaru 90 mai suna Yusuf Yarkadir ga shiga hannun hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) a kan siyar da kwayoyi ga matasa a kauyensu mai suna Yarkadir a karamar hukumar Rimi ta jihar.

Yayin da aka tuhume shi, tsohon ya sanar da cewa shi ke siyarwa matasan yankin wiwi na tsawon shekaru takwas, Daily Trust ta ruwaito.

Tsoho mai shekaru 90 ya shiga hannun NDLEA kan safarar miyagun kwayoyi

Kamar yadda mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya sanar, duk da wanda ake zargin ya kasa bayyana inda yake samun kayansa, ya sha alwashin barin irin harkar duk da ya so hakan a baya.

Har ila yau, jami'an hukumar NDLEA na jihar Ondo sun damke wasu 'yan uwa biyu tare da sauran wadanda ake zargi da zama dilolin miyagun kwayoyi a babban birnin jihar.

Matasan da aka kama sune: Onyema Sunday mai shekaru 16 da 'yar uwarsa Onyema Amaka mai shekaru 15 an kama su a Car Street dake yankin Akure dauke da 1.9kg na Tramadol a ranar Litinin, 5 ga watan Yuli.

An kama Kazeem Oluyede mai shekaru 23 a yankin Eru Oba dake babban birnin jihar dauke da 300g na wiwi da 3g na methamphetamine, Daily Trust ta wallafa.

Hakazalika, Maryam Musa mai shekaru 35 ta shiga hannu a yankin Igbara-Oke dake karamar hukumar Ifedore ta jihar dauke da 5.5kg na wiwi duk a rana daya.

A wani labari na daban, hukumar kula da lamurran 'yan sanda (PSC), a ranar Alhamis ta yi watsi da kudirin karin girma ga tsohon mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Ibrahim Magu.

Hukumar ta ce tana jiran umarni daga ofishin antoni janar na tarayya da ministan shari'a tare da sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Daily Trust ta wallafa.

Wannan sanarwan na kunshe a wata takarda da aka baiwa manema labarai ta hannun kakakin hukumar, Ikechuckwu Ani.

Source: Legit.ng

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN