Talakawa na son Buhari: Fadar shugaban kasa ta ce PDP ta cire rai a zaben 2023


Fadar Shugaban kasa a ranar Talata ta fada wa babbar jam’iyyar adawa ta PDP, da ta daina sa ran lashe babban zaben na 2023, saboda har yanzu talakawa za su yi wa Shugaba Muhammadu Buhari mubaya'a kuma ba za su taba yin watsi da shi ba.

An zargi PDP da ba ‘yan Najeriya fatan karya cewa saboda rashin tabuka abin a zo a gani a jam’iyyar APC, a matakin kasa, cewa (PDP) za ta karbi mulkin da ta rasa a hannun APC a shekarar 2023, Daily Nigerian.

Amma Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu, wanda ya yi magana jim kadan bayan Sallar Idi a Daura ta Katsina, ya ce ’yan Najeriya sun sani daram kuma ba za su yarda wani bangare ya karbi mulki a 2023 ba.

A cewarsa:

"Shugaban yana da goyon baya mara girgiza ba kawai a mahaifarsa ba har ma a duk fadin kasar kuma ya isa ga ‘yan adawa su yarda cewa Shugaban kasar yana da matukar muhimmanci ga jam’iyya mai mulki da 'yan Najeriya baki daya.

“Har ilayau, ya zama musu cikas ga siyasa da ba za su iya wargazawa a zaben 2023 ba.

"Mun yi imanin cewa PDP da sauran jam’iyyun adawa suna bakin ciki da fatan karya kan mulki a zaben 2023.

“Talakawa ba za su taba yin watsi da shugabancin Shugaba Buhari da APC ba. Ina tabbatar muku da cewa a 2023, talakawa za su jira Shugaban kasa ya nuna hanya cikin ladabi da abi da ya gina wa kasa ta fuskar samar da ababen more rayuwa da kuma jin dadin matasa a kasar.

"Babu wanda zai dauki kasada ta hanyar gayyatar wani bangare ya zo ya karbi mulki a 2023."

Matashi daga jihar Kano zai tsaya takarar shugaban kasa a APC, ya gana manya kan batun

Wani matashi dan shekaru 35 da ke neman tsayawa takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam’iyyar APC a jihar Kano, Malam Aminu Sa’idu, a jiya ya gana da mataimaka na musamman (SAs) ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje don sanar da su burinsa.

Da yake magana da Daily Trust bayan ganawar, matashin ya ce yana daga cikin shawarwarin da yake bi gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Ya kuma ce ganawar ta yi daidai da kudirin dake rajin ba matasa damar a dama dasu a mulki na"Not Too Young to Run", da kuma dabarun fadada aniyarsa zuwa dukkan sassan kasar.

A wani labarin, Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bai wa sojojin da suka ji rauni da ke yaki a yankin tallafin naira miliyan 10 a jiya Talata.

Yadda na zama Alkalin mukabalar Abduljabbar Kabara da Malamai inji Salisu Shehu

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya sanar da ba da tallafin ne a yayin liyafar cin abincin rana da babban hafsan sojin kasa na Najeriya Manjo Janar Farouk Yahaya ya shirya a Barikin Maimalari da ke Maiduguri.

Gwamna Zulum ya yaba wa dakarun kan jajircewarsu da kuma jaddada alkawarin gwamnatinsa na ci gaba da ba su goyon baya har a cimma nasara a yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya a yankin.

Source: Legit.ng

Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari