Rundunar sojin Najeriya ta karyata sakin 'yan Boko Haram, ta fayyace gaskiya

 


A ranar Alhamis din da ta gabata ne Sojojin Najeriya suka karyata rahotannin sakin mayakan Boko Haram da aka kama a Borno, Daily Nigerian ta ruwaito.

Wata sanarwa dauke da sa hannun Onyema Nwachukwu, Darakta, Jami’in Hulda da Jama’a na Soji, ta ce rahotannin karya ne kuma wani mummunan yunkuri ne na dakile tarbiyyar sojoji da kuma tozarta sojojin na Najeriya.

Ya ce rundunar Soji ba ta da niyyar shiga batutuwa tare da wadanda suka kitsa labaran na karya amma za su yi kokarin daidaita bayanan.

Sanarwar ta ce:

“An sanar da Sojojin Najeriya (NA) game da wata kafar yada labarai da ke zargin cewa NA ta mika tsoffin mayakan Boko Haram 1009 ga gwamnatin jihar Borno.
“Rahoton ya kuma yi zargin cewa an yi taron sakin cikin sirri. Wannan rahoton a bayyane yake yana daya daga cikin irin kokarin da ake yi na dakushe kokarin sojoji da kuma tozarta NA, ta hanyar ba da rahotannin da ba su da tushe da kuma bayanan da ba su dace ba."
"Ba shakka cewa ayyukan da ake yi na magance kayar baya da ta'addanci (CTCOIN) a yankin Arewa maso Gabas ya kai ga kame wadanda ake zargi da ta'addanci / masu tayar da kayar baya."
“Wadannan da ake zargin an tsare su a yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike da kuma karin bincike daga masana na Cibiyar Bincike ta Hadin Gwiwa (JIC).
"Kuma wadanda aka samu da laifi galibi ana mika su ga hukumomin da ke gabatar da kara a kan haka, yayin da wadanda ba su da hannu a ta’addanci da tayar da kayar baya ana wanke su kuma a sake su ga gwamnatin jihar domin gyara su kafin a maida su cikin al'umma.
“Saboda haka wadannan wadanda ake zargin ba tsoffin mayakan Boko Haram ba ne, kamar yadda aka yi ta yadawa a rahotonni da aka fitar a yanar gizo kamar yadda aka kitsa makircidon nuna wa jama’a.
“Saboda haka an saki jimillar wadanda ake zargi 1009, ba tsoffin mayaka ba, saboda haka aka sake su bayan tsaurara matakan bincike a ranar Laraba 14 ga Yulin 2021.
“Har ila yau ya zama dole a bayyana karara cewa mika wadanda ake zargin ba a yi shi cikin sirri ba kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyoyin agaji suka shaida, tare da kyakkyawan tsarin duniya.
"Don haka, NA take kira ga jama'a da su yi watsi da wannan karairayi, domin a bayyane yake kirkira ne da murde gaskiyar abinda ya faru."

Hukumar Sojoji ta saki yan ta'addan Boko Haram 1009, ta mikasu ga gwamnatin Borno

A baya rahotanni sun ce, hukumar Sojin Najeriya a ranar Laraba ta saki tsaffin yan Boko Haram 1,009 da suka kasance hannun Sojin a barikin Giwa dake Maiduguri, birnin jihar Borno.

An mikawa gwamnatin jihar Borno wadannan tsaffin yan ta'addan ne a wani taro na sirri da aka shirya yi a baya amma aka dage saboda mutuwar tsohon shugaban hafsin Soji, Punch ta ruwaito.

A cewar wasu majiyoyi dake cikin gidan Soja, an mika yan ta'addan ga kwamishanar harkokin mata, Hajiya Zuwaira Gambo, wacce ta wakilci gwamnatin jihar.

Sojojin saman Najeriya sun ragargaji 'yan ta'addan ISWAP, sun kwato makamai

A wani labarin, Dakarun sojin saman Najeriya sun lalata manyan motocin bindiga guda uku mallakar ‘yan kungiyar ta’addanci ta ISWAP yayin da suke tsallaka hanyar Damaturu zuwa Maiduguri domin aikata barna kan mazauna yankin, Daily Trust ta ruwaito.

Da yake yi wa manema labarai karin bayani a hedikwatar tsaro da ke Abuja ranar Alhamis kan ayyukan sojoji a cikin makonni biyu da suka gabata, Mukaddashin Daraktan, Harkokin Watsa Labarai na Tsaro, Brig Benard Onyeuko, ya ce sojojin sun kashe duk wadanda ke cikin motocin.

Onyeuko ya bayyana cewa, sojojin na sama, wadanda suka gudanar da ayyukan ta amfani da jirage masu saukar ungulu NAF Mi-35, sun yi aiki ne a lokacin da suka samu kiran gaggawa tare da tabbatar da cewa an kwato dukkanin makaman ‘yan ta’addan a yayin samamen.

Source: Legit Newspaper

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN