Rahoton tsaro: Yadda 'yan Boko Haram suka kai hari sansanin sojojin Kamaru


Jaridar Legit ta rewaito cewa Mayakan Boko Haram sun mamaye wani sansanin sojoji a yankin Arewa mai nisa na Kamaru a ranar Asabar 24 ga watan Yuli, 2021, inda suka kashe a kalla sojoji bakwai tare da jikkata wasu da dama, in ji majiyar sojoji wasu da daban.

Sun buge sansanin da ke yankin Sagme da misalin karfe 4.00 na safiyar ranar Asabar, kamar yadda sojoji biyu da wani mazaunin yankin suka shaida wa Xinhua.

Maharan, wadanda ke dauke da muggan makamai, wasu daga cikinsu cikin shigar sojoji sun zo ne cikin jerin gwanon motoci shida, in ji wani soja.

Bayan an kwashe sa’o’i ana fada, an kashe kwamandan sansanin sojoji tare da abokan aikinsa shida.

Wani soja da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa:

“Sojojin sun nuna jarumtaka kuma sun kare kansu da karfi."

“Abun godiya ne saboda sun sami nasarar fatattakar maharan kuma sun ceci rayuka da yawa."

Sojan ya kara da cewa har yanzu ba a san adadin rayukan da sojoji suka mika lahira daga bangaren 'yan ta'addan ba.

'Yan Boko Haram sun addabi sojojin Kamaru

Harin na ranar Asabar shi ne mafi muni a kan sojojin Kamaru a cikin sama da watanni 10, a cewar rahotannin tsaro.

Kungiyar Boko Haram ta addabi yankin Arewa mai nisa na Kamaru tun daga shekarar 2014, inda suka kashe mutane sama da 2,000, a cewar rahotannin tsaro, The Guardian ta ruwaito.

A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta ce mayakan Boko Haram da na ISWAP 28 da iyalansu da suka tsere sun mika kansu ga dakarun rundunar bataliya ta 151 a jihar Borno.

Mai magana da yawun rundunar sojin Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Laraba, BBC ta ruwaito.

Sanarwar ta ce mayakan da suke tsere wa hare-haren sama da ake kai musu sun mika wuya ne ga dakarun bayan da aka fi karfinsu.

Source: Legit.ng

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN