NDLEA Ta Cafke Dillalan Kwayoyi 89 da Tan 2,800 Na Haramtattun Magunguna a Kebbi


Yunkurin yaki da muggan kwayoyi a shekarar 2021 ya shafi 'yan sanda ne na Birnin kebbi da kuma duba matsalar ta'ammali da miyagun kwayoyi da fataucinsu ta barauniyar hanya, da nufin rage irin wannan zuwa mafi karancin abu da kuma karfafa tsaro a jihar.

“Daga watan Janairu zuwa 7 ga watan Yuli, an cafke wadanda ake zargi 89; a cikinsu, 87 maza ne yayin da biyu ne kawai mata.

“Hakanan, an kama tan 2,800 na magunguna da fitar da su daga wurare daban-daban; kuma wasu daga cikin wadannan jami'an Kwastam na Najeriya (NCS) da kuma 'yan sandan

A cewarsa an kame tabar wiwi da ta kai kilogram 2,594.6016, kwayar tramadol, diazepam da maganin tari mai dauke da hodar iblis da suka kai kilogram 232.2947.

NDLEA Ta Kwamushe Wata Mata da Hodar Iblis 100 Kunshe Cikin Al'aurarta

Jami'an hukumar NDLEA sun cafke wata 'yar Najeriya da ke zaune a kasar Brazil, Misis Anita Ugochinyere Ogbonna, a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe (NAIA) dake Abuja, dauke da kwalayen hodar iblis 100 da ta boye a al'aurarta da jakarta.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya fada a ranar Lahadi a Abuja cewa an kama matar mai 'ya'ya uku ne a daren Juma’a lokacin da suka isa Abuja ta jirgin Qatar Air daga Sao Paulo na Brazil ta Doha babban birnin kasar Qatar.

A cewarsa, yayin binciken kwakwaf, an ciro hodar iblis 12 da ta saka a al'aurarta yayin da aka gano wasu kunshi 88 da aka saka a cikin safa a boye cikin jakarta, Daily Trust ta ruwaito.

Badakala: Shugaban EFCC Ya Ci Alwashin Gurfanar da Wani Babba a Jami'iyyar APC

A wani labarin daban, Shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya sha alwashin cewa hukumar za ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Bawa ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 17 ga watan Yuni.

Kalu, wanda yanzu haka dan majalisar dattijai ne, Kotun Koli ta sake shi a kan ka'idoji bayan an same shi da laifin satar biliyoyin nairori lokacin da yake gwamnan jihar Abia tsakanin 1999-2007.

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN