Na bar tallata kayan ƙawa ne saboda ba na son cire hijabina' - Halima Aden


BBC Hausa ta ruwaito cewa, lokacin da Halima Aden, wadda ita ce mace mai sanya hijabi ta farko wadda kuma ta shahara kan tallata kayan ƙawa, ta daina aikin a bara, ta yi haka ne saboda mata Musulmi ba za su sake fuskantar yin zaɓi tsakanin addininsu da aikinsu ba.

"Ina son 'yan mata su san cewa Halima ta ɗauki matakin kariya guda dominsu," a cewarta.

"Na ajiye aikina saboda su samu zarafin kin amincewa a duk inda suka ji lamarin bai yi musu ba."

A halin yanzu, wasu manyan masu gidajen tallata kayan ƙawa da na kwalliya na duba yadda za a kiyaye matsa wa mata Musulmi masu tallata kayan ƙawa da na kwalliya kamar yadda aka yi wa Halima.

"Ina ganin wannan ya kasance matashiya ga masana'antar nan saboda sauran masu kamfanonin tallata kayan ƙawa na cewa me muka yi ne da ya kasance ba daidai ba?" in ji Tommy Hilfiger mai zanawa da haɗa kayan ƙawa.

Halima Aden and Tommy Hilfiger

Ya yi aiki sosai tare da Halima a wasu bukukuwan tallar kayan ƙawa kuma shi da ita sun yi wata ganawa da BBC, domin tattaunawa kan bukatar kawo karshen nuna bambancin launin fata da ya yi yawa a masana'antar.

'Hijabina sai ƙara ƙanƙancewa yake yi'

"Na kai matakin da na fara sakin layin ainihin wace ce ni kuma girman hijabina na ta raguwa," in ji Halima.

"Wata rana ina wajen daukar shiri sai na ga wata yarinyar ita ma da hijabi. Sai suka ba ni akwatina da kayan adona ke ciki, ita kuma sai aka ce mata ta je ta nemi ban-daki ta shirya. To da na ga yadda aka nuna bambanci a tsakaninmu sai na ji abin bai min dadi ba.

Sannan akwai wata ranar aka ce ta shiga wani waje ta shirya wanda yake dab da inda maza ke shiryawa.

"Lamarin ya sa na kasa samun sukuni sam," a cewar Halima.

"Ina jin bacin rai matuka na ji wasu masu yi mana kwalliya, ko wasu mutanen na son sauya ka daga yadda kake. Kuma ina ga hakan matsala ce sosai ga fannin tallata kayan kawa," kamar yadda Tommy ya shaida wa Halima.

Tommy Hilfiger yana yawan yin kira kan nuna daidaito a masana'antar tallata kayan kawa. A shekarar 2020 ya yi alkawarin bayar da dala miliyan 15 cikin shekara uku don a kara yawan sanya mutane daga bangarori daban-daban cikin harkar.

Shi ne mai kamfanin fitattun kaya na farko da ya sanya Halima ta fara tallata kayan kawa a bikin Paris Fashion Week.

Ita ce kuma ta farko da ta fara sanya kayan ninkaya da aka wallafa hotonta a wata Mujallar Wasanni, a lokacin da ta sanya kayan masu rufe jikinta wanda kamfanin Tommy Hilfiger ya yi.

"Na tuna yadda muka yi miki kayan ninkaya masu suturta jiki," in ji Tommy.

Sanya kayan ninkaya na burkina abu ne da ba zan manta da shi ba," a cewar Halima.

Halima Aden

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

"Akwai kasashe irin su Faransa da suka haramta sanya su a wuraren taruwar jama'a kamar bakim teku. Don haka ina jin sanya hoton a shafin Mujallar Wasanni abu ne mai kyau."

'Harzuka mutane'

"Ina jin kamar a kan siradi nake tafiya, kuma kamar zan harzuka mutane musallan al'ummar Musulmai a wasu lokutan," in ji Halima.

Ina yawan samun sakonni cewa 'Wannan kayan ruwan na mata suna kama jiki sosai.' Amma wasu kuma suna yawan cewa: 'Muna so mu ganki a shiga ta da daban. Muna so mu ganki cikin hijabi na musamman.

"Kayan na da dadin tafiya saboda rashin kaurinsa."

BBC ta yi magana da Tommy da Halima: fitattun masu tallace-tallace daga sassa daban-daban wadanda suka amince su ba da labarinsu da gwagwarmayarsu game da masana'antar kwalliya.

Halima Aden

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Ramla Ossoble, Musulma ce mai shekara 22 mai harkar tallace-tallace, wadda ta bayyana cewa mutane da dama da ta yi aiki da su ba su fahimci cewa akwai yanayin kwalliyar da addininta ya hana ba.

"Masu kamfanin kwalliya sun sha tambaya ko zan sa matsattsun kaya, inda muke gardama sosai a kai saboda ina fada musu cewa ba zan iya sanya kayan da suke nuna jikina sosai ba," in ji ta.

"Akwai wani lokaci ma da wani mai daukar hoto ya ce ko zan iya canja kaya a cikin tasha, wanda ya matukar ba ni mamaki."

A wajen Halima, wadda ta shama fama da kamfanonin ado akan irin wannan abubuwan, ta ce, "akwai takaici yadda kamfanonin adon nan suka gaza gane cewa akwai masu tallata haja da suke amfani da hijabi wadda kuma ba za ta samu sukuni ba idan ta sa matsatstsun kaya," in ji ta.

Lokacin kawo sauyi

Shi ma Tommy yana fama da irin damuwar da su Ramla suke ciki, wanda hakan ya sa ya kuduri aniyar magance matsalar wariyar da ake nuna wa irinsu.

"Gaskiya lamarin akwai ban haushi da rainin wayau, wanda yake matukar ba ni haushi," in ji ta.

"Akwai takaici ya kasance kana cikin al'umma ko kasuwanci da zai kasance akwai sharuda marasa kan gado.

"Ina da burin zama jagorar kawo sauyi. Sannan ina da burin ganin an faro sauyin daga sama."

Kamfanonin tallace-tallace na duniya sun kuduri aniyar tafiya da kowace irin al'ada a duk matakan harkokin kamfanoninsu.

Amma sai dai a wata kididdiga da aka yi a wani binicke da Kamfanin McKinsey game da mata a wajajen aiki, an gano cewa kusan uku cikin hudu na daraktocin kamfanoni Turawa ne.

Kaeleen Stammers, wata mai tallata haja bakar fata mai shekara 23 ta nuna sha'awar ganin abin da Tommy ke yi domin samun wakilcin mata a kowane bangare.

"Na sha samun sabani mai karfi tsakanina da daraktocin da muka yi aiki da su da kamfanonin talla da suke fada min cewa yarinya kaza ba za ta iya zama babbar mai tallace-tallace ba saboda wasu dalilai.

"Ni kuma nakan ce musu, ni ce oga, don haka idan za ku min aiki ni zan fadi abin da nake so da yadda za a yi."

Taron nuna kwalliya na bana ya fi sauran na baya girma da fadada, inda aka samar da kusan kashi 43 na aiki ga masu tallace-tallacen kaloli.

A shekarar 2020, kusan rabin mujallun duniya sun yi bayani ne game da masu tallace-tallacen kaloli, wanda ya nuna karin kashi 12 akan shekarun baya.

Sai dai amma kashi! Samun karin har yanzu bai amfanar yadda aka zata ba.

A Birtaniya, daya cikin 10 na ma'aikatan kamfanonin kwalliya masu tallace-tallaceb kala ne.

Halima Aden on the red carpet

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Tommy ya ce yana kokari wajen tabbatar da cewa kamfaninsa ya yi kokari wajen tafiya tare da kowa a bayyane da bayan fage.

"Ina so in zama wanda ya tabbatar da hakan a aikace ba kawai magana ba.

Sai dai na san ba zan iya yi ni kadai ba, burina shi ne a samu sauyi a harkar baki daya.

Ba wai maganar masu tallata ba ce, magana ce ta gyara a bangaren baki daya."

'Ina so mu riga taimakon junanmu'

Halima tana alfahari da kawo sauyi a bangaren, inda ake amfani da kaya masu rufe jiki wajen kwalliya a duniya da kuma kasancewarta abar koyi wajen mata masu amfani da hijabi wajen tallace-tallace.

"Lokacin da na kuduri aniyar fara tallace-tallace, abin da ya zo min a zuciya shi ne wannan lamarin zai bude wa wasu mata hanya a yankinmu. Ban taba tsammanin zan bude mujalla ba in ga mace sanye da hijabi."

Amma sai dai duk da daukakar da ta samu, Halima takan yi tunanin cewa harkar ba ta dace da mata Musulmi ba.

Hakan ya sa take da burin kawo canji a harkokin.

"Ina kokarin duba wasu bangarorin da babu mata Musulmi da yawa a ciki, da kuma ganin yadda zan kawo canji kamar yadda na samu nasarar kawo sauyi a masana'antar kwalliya.

Misali, na fara tunanin yadda zan kawo canji a masana'antar fim, da rubuta littafan yara game da matsalolin da ake fuskanta a sansanonin gudun hijira."

Halima na so ta samu karin bayanai game da tafiya da kowace al'ada a harkar kwalliya.

"Babban burina shi ne a tafi tare da kowa.

Ina so mu taimaki juna sannan mu kasance masu gaskiya wajen tafiyar da al'amuranmu a ciki da wajen harkar ta tallace-tallace.

"Na hango cewa akwai damammaki da dama a masana'antar kwalliya."

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN