Hotunan yadda aka kama wadanda suka kashe shugaban kasar Haiti da abin da ke faruwa da su yanzu


Mahukunta a kasar Haiti sun kama wasu Yan kasar Amurka guda biyu da Yan kasar Colombia guda 17 bisa zargin kashe shugaban kasar Haiti Joveneil Moise.

Wadanda ake zargi sun yi wa shugan Haiti Juvenel da matar shi Lady Martine ruwan harsashi 12, lamari da ya sa kwayan idon shugaban kasar guda daya ya fito kuma ya mutu, matarshi ta sami munanan raunuka. 

Daga cikin wadanda aka kama har da James Solages, mai shekara 35, da Joseph Vincent, duk yan kasar Amurka amma suna da asalin haihuwa a kasar Haiti. Sauran wadanda aka kama su 15 yan kasar Colombia ne. An kma su ne bayan mumunan harin na ranar Laraba a fadar shugaban kasar da ke tsaunukan Port-au-Prince. 

Shugaban yansandan kasar Haiti Léon Charles, ya ce maharan guda uku ne kawai yansanda suka kashe ba kamar yadda aka labarta a baya ba. Ya ce mutum 8 cikin maharan sun tsere. Ya tabbatar da fuskokin wadanda aka kashe da wadanda suka tsere bayan an gano su ta takardar Fasfo nasu.







إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN