Gwamna Abdulrazaq da Saraki sun yi watsi da junansu a filin Idi


Wannan shi ne karo na farko da Saraki zai yi Sallar Idi a Ilorin tun bayan bayyanar Abdulrazaq a matsayin gwamnan jihar.

Abdulrazaq da jam’iyyar All Progressive Congress (APC) sun fatattaki Saraki da Peoples Democratic Party (PDP) ta hanyar "juyin juya halin O'toge".

Saraki ya isa Ilorin kwanaki hudu da suka gabata, inda ya karbi bakuncin wasu abokansa da dama.

Mutane da yawa sun yi tsammanin tsohon gwamnan na jihar zai tashi daga Ilorin kamar yadda ya yi a lokacin bikin Eid-el-Fitri da ya gabata domin kaucewa rikici tsakanin magoya bayansa da na Abdulrazaq.

Babu kyakkyawar jituwa a tsakanin shugabannin biyu.

Amma ya ba mutane da yawa mamaki yayin da ya iso filin Sallar Idi da misalin karfe 8:30 tare da wasu hadimansa da tsofaffin masu rike da mukaman siyasa wadanda ke masa biyayya.

Daga cikinsu akwai tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Alhaji Kawu Baraje, da tsohon Shugaban Majalisar Dokoki, Dokta Ali Ahmad.

Jaridar ta kuma tattaro cewa Gwamnan ya iso yan mintuna kadan amma yayi biris da shugaban majalisar dattijan.

Tsohon Babban Alkalin Najeriya, Mai shari’a Moddibo Alfa Belgore, Darakta-Janar na Cibiyar Nazarin Dokoki ta Kasa, Farfesa Abubakar Sulaiman, dan takarar Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Mallam Saliu Mustapha, tsohon babban alkalin kotun musulunci, Justis Salihu Olohuntoyin Mohammed, na daga cikin manyan mutane a filin addu’ar.

Source: Legit

Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari