Duba dalili da ya sa EFCC ta daskarar da asusun bankin 'yar majalisa bayan ta siya motar N1bn


Daga cikin binciken siyan motocin da majalisar jihar Oyo tayi, hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta daskarar da asusun bankin daraktan kudi da asusu na majalisar jihar.

Tribune Online ta ruwaito cewa EFCC ta daskarar da asusun bankin daraktan kudi ta majalisar wacce ta ki amsa gayyatar da hukumar tayi mata.

Daskarar da asusun bankin na hana mutum cire kudi daga asusun bankinsa gaba daya.

Ana zarginsu da siyo tsoffin motoci a matsayin sabbi

Daraktan tana daya daga cikin jami'an majalisar da ake tuhuma bayan an mika wani korafi na cewa kakakin majalisar ya hada kai da wasu jami'an gwamnati wurin samar da tsoffin motoci a matsayin sabbi ga 'yan majalisar.

Kamar yadda Tribune Online ta wallafa, wani jami'in hukumar EFCC ya ce daga bisani daraktan kudi ta majalisar ta bayyana bayan daskarar da asusunta na banki da aka yi.

Tsageru sun kashe DPO a Imo

'Yan bindiga da ake zargin tsagerun IPOB ne sun sheke CSP Fatmann Dooiyor. Dooiyor wanda shine babban jami'in dan sanda a Omuma, garinsu Gwamna Hope Uzodimma dake karamar hukumar Oru ta gabas dake jihar Imo.

Gagararrun 'yan bindiga sun tsinkayi babbar kotun tarayya dake Abuja inda aka gurfanar da Nnamdi Kanu. Jami'an DSS basu kai shi kotu ba, lamarin da yasa aka dage shari'ar zuwa watan Oktoba, Daily Trust ta wallafa.

Kamar yadda takardar da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Imo, CSP Mike Abattam ya fitar, yace 'yan sanda sun sheke shida daga cikin 'yan bindigan kuma an cafke 11 daga cikinsu.

Source: Legit.ng

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN