Hotuna: Duba Budurwa da ta ce ta fi kowa manyan labban baki a fadin Duniya


Wata daliba da ta yi ikirarin cewa ita ce ta fi kowa manyan labban baki a fadin Duniya ta bayyana aniyarta na sake ziyartar kwararru domin a kara cika mata labbanta saboda su kara girma.

Yar shekara 23 a Duniya, Andrea Ivanova, yar asalin kasar Bulgaria, ta je kwararru suka cika labban bakinta da sinadarin hyaluronic acid fillers a 2018. Kuma yanzu haka tana ziyartar kwararru domin a kara wannan sinadari kowane wata.

Ta shaida wa Daily star cewa tana jin dadin ganin yadda labbanta suka zama, kuma hakan na faranta mata rai, duk da cewa Iyaye da Yan uwanta basu goyi bayan hukuncin da ta dauka na sa labbanta su girma ba, kuma sun tsani ra'ayinta.

Ta ce " An yi mani allura 25 na hyaluronic acid a labbana. Sai dai ban duba adadin nawa na kashe wajen yin allurar ba. Amma kowane allurar hyaluronic acid a nan kasar Bulgeria ana sayar da shi a kan Leva 400 kimanin Pan 200 kudin kasar Ingila.

Sakamakon haka ta kashe kimanin Pan £5,000.a allura 25.Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN