Duba abin da Yan Banga suka yi ma wani barawon wayoyin transfoma


Yan Banga sun cafke wani ƙasurgumin barawo bayan ya saci manyan wayoyin wutan lantarki a Eket da ke jihar Akwa Ibom.

An cafke wannan barawo ne a kan hanyar Edem Udo da Afaha Uqua a garin Eket ranar Lahadia 11 ga watan Yuli.

Rahotanni sun ce wanda aka kama ya sha sace wayoyin wuta daga transfoma a yankin, lamari da yake jefa al'umman yankin cikin duhu sakamakon rashin wutan lantarki.

Al'umman garin sun lafta mashi na jaki har ya yi laushi, daga bisani suka zagaya da shi cikin gari domin su kunyata shi. Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN