Dalilin da ya sa gwamnatin Najeriya ba ta biya wasu cikin matasa 774,000 haƙƙinsu ba


A farkon watan Janairun bana ne gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da wani shiri na musamman domin sama wa matasa 774,000 aikin yi na wucin gadi don rage masu radadin tattalin arziki da annobar korona ta haifar.

An dauki mutum 1,000 ne daga kowace karamar hukuma a fadin kasar.

Galibi an dauke su aikin shara, da kula da makarantu, da magudsnan ruwa da kuma sa ido kan muhimman kayayyakin more rayuwa na gwamnati gwargwadon bukatun yankin da suke aikin.

Aikin na tsawon watanni uku ne inda za a riƙa ba su kudaden alawus.

Shirin da aka yi wa laƙabi da Special Public Works yana cikin jerin tsare-tsare da gwamnatin Najeriya ta ɓullo da su da nufin taimaka wa talakawa wajen sauƙaƙa musu matsin rayuwa.

Matasa marasa aikin yi, da naƙasassu, da mata da masu ƙananan sana'o'i na cikin wadanda aka bullo da tsare-tsaren dominsu.

To sai dai akwai korafe-korafe na cewa har yanzu da dama daga cikin matasan da aka bai wa aikin yi na wucin gadi na watannni uku, ba a biya su hakkokinsu ba.

Mene ne ya hana biyan haƙƙokin masu ƙaramin ƙarfin?

Dama gwamnatin Najeriya ta yi alkawarin biyan kowane matashi da aka bai wa aikin wucin gadin albashi ko alawus na naira 20,000 a wata - wato duk wanda aka bai wa aikin zai samu naira 60,000 cikin watanni uku.

To amma rashin biyan da dama daga cikinsu haƙƙoinsu, ya sanya wasu na ganin burin shirin na rage radadin tattalin arziki ya gamu da nakasu, murnar wasu da aka ba aikin kuma na neman komawa ciki.

Shugaban hukumar samar da ayyukan yi ta kasa a Najeriya wato NDE Malam Abubakar Nuhu Fikpo, wanda ke jagorantar shirin, ya shaida wa BBC cewa tangardar da aka samu wajen asusun banki na matasan da aka bai wa aikin ne.

Sai kuma alamun aringizo da aka gani, su ne manyan dalilan jinkiri wajen biyan wasu daga cikin ma'aikatan haƙƙoƙinsu.

Malam Abubakar Fikpo ya ce ''misali za ka ga sunan mutum guda ya fito a bankuna daban-daban.''

Ya kara da cewa duk da kokarin da suke yi na tabbatar da gaskiya, ga alama wasu na yunƙurin dagula lamura ta hanyar kokarin aringizo ko kuma karbar kudin alawus da ba su cancanci su karba ba.

Shugaban ya ce yanzu haka hukumar da kuma bankuna a fadin Najeriya na aiki tare kuma tukuru domin warware matsalar da ake fuskanta.

Ya ce ''muna nan muna kan tantancewa'' domin biyan wadanda ba a biya su ba.

Shugaban NDE ɗin ya ce akwai babbar illa muddin aka biya matasan ba tare da an tantance ba, kuma akwai yiwuwar a yi rashin adalci.

Ya yi nuni da cewa, rashin tantancewa ka iya sanya wasu su kasa samun kudadensu har abada.

A cewarsa, ''lallai da mun biya kai tsaye, da mun kwan ciki. Don da mun biya wasu fiye da yadda ya kamata mu biya, wasu kuma sai su tashi a tutar babu.''

Yaushe za a biya matasan?

Shugaban Hukumar Samar da Ayyukan Yi ta kasa NDE, Malam Abubakar Nuhu Fikpo, ya shaida wa BBC cewa ana kan tantance wadanda ba a biya su ba.
Bayanan hoto, Shugaban NDE Malam Abubakar Nuhu Fikpo, ya shaida wa BBC cewa ana kan tantance wadanda ba a biya su ba

Su kansu mahukunta dai sun tabbatar da cewa bai kamata a ce ba a biya matasan ba, musamman wadanda aka ba aikin kuma suka yi.

Wasunsu sun dade da kammala aikin amma kudadensu bai shiga aljihunsu.

Hukumar NDE ta ce kawo yanzu kimanin kashi 40 cikin 100 ne na wadanda aka bai wa aikin ba su samu kudadensu na alawus ba.

Ga wadanda ba a biya su hakkin nasu ba, babban abin da suke fata shi ne a biya su.

Shugaban NDE, Malam Abubakar Fikpo ya ce ''a cikin kashi 100, mun cimma kashi fiye da 60'' wajen aikin biyan matasan.

Ya bayar da tabbacin cewa ana gab da biyan sauran, domin su ma ba sonsu ne a ce har yanzu ba a biya mutanen da suka yi aiki ba.

Ya shaida wa BBC cewa ''in Allah Ya yarda, nan da sati hudu ko wata daya za mu iya mu kammala biya, domin mutane sun riga sun yi aiki, biya ne ya yi saura.''

Ya kuma ce sun bukaci bankuna su tabbatar sun gyara duk wata matsala da ta shafi lambar tantance sahihancin asusu wato BVN, sannan su mika wa hukumar sunayen wadanda aka tantance kuma aka tabbatar da sahihancinsu domin a biya su hakkinsu nan take.

Hukumomi sun ce aikin biyan kudaden alawus din na ci gaba da gudana.

Wasu labarai masu alaka:

Akwai yiwuwar a sake daukar wasu ɗumbin matasan aiki

Najeriya kasa ce da matsalar rashin aikin yi da talauci suka yi wa jama'a katutu - musamman tsakanin mata da matasa.

Duk da cewa gwamnatin Najeriya ta ce kashin farko na shirin samar da aikin na wucin gadi ya yi tanadin daukar matasa kimanin 774,000 a fadin Najeriya, miliyoyin matasa na ci gaba da fama da matsalar rashin aiki.

Hatta wadanda aka dauka karkashin wannan shirin, dama aikin nasu na wucin gadi ne don rage radadin talauci da korona ta ta'azzara.

Shugaban hukumar ta NDE ya ce dama shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba su umarnin su tabbatar sun aiwatar da shirin don rage ''wahalhalun da mutane ke fuskanta.''

Malam Abubakar Fikpo ya ce idan aka kammala wannan kashi na aikin, to hukumar ta NDE zata mika rahoto ga Karamin Ministan Kwadago, Festus Keyamo, wanda shi ne shugaban kwamitin gudanarwa na shirin.

Daga nan ne za a yi nazari domin daukar mataki na gaba kan makomar shirin.

To amma babban jami'in samar da ayyukan yin na Najeriya ya nuna kwarin gwiwar cewa shugaba Muhammadu Buhari zai amince a ci gaba da gudanar da shirin a fadin Najeriya bayan kammala kashin na farko.

A cewar Malam Fikpo ''muna kyautata zaton cewar ganin yadda mutane suka karbi wannan aikin, ba mamaki shugaban kasa ya sake ba mu dama mu kuma maimaita wannan programme din (shirin) domin mutane su amfana.''

Rahotun BBC

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN