Dalilin da ya sa Buhari zai je Kano da yadda zuwansa zai shafi jama'a da yan kasuwa


Nan gaba a ranar Alhamis ne ake sa ran Shugaban Najeriya Muhammad Buhari zai ziyarci jihar Kano da ke arewacin kasar domin kaddamar da ginin sabon layin dogo daga jihar zuwa Kaduna.

Ana sa ran sabon layin dogon zai hade da na jihar Kaduna zuwa Abuja, da wanda ya taso daga Abuja zuwa Lagos.

Jihar Kano ita ce cibiyar kasuwanci arewacin Najeriya inda 'yan kasuwa daga sassan kasar daban-daban har ma da sauran kasashen duniya ke zuwa domin yin hada-hadar kasuwanci.

Sai dai harkar sufurin jiragen sama a jihar ta jima da durkushewa, inda 'yan kasuwa suka fi mayar da hankali wajen dakon kayansu a manyan motoci daga jihar zuwa wata, ko kuma daga wata jihar zuwa Kano.

Yadda aikin zai shafi 'yan kasuwa

'Yan kasuwar Kano sun ce aikin zai taimake su

ASALIN HOTON,GOOGLE

Bayanan hoto,

'Yan kasuwar Kano sun ce aikin zai taimake su

Abdullahi Musa Mai siminti, wanda a baya yake dauko simunti daga Gombe da Lagos ta jirgin kasa zuwa Kano, ya shaida wa BBC cewa rashin layin dogon ya sa harkokin kasuwanci sun kara wahala kuma hakan na daga cikin dalilan da suka janyo tashin kayayyaki.

Shi ma Nasir Shehu Haske, wanda a baya yake harkar daukowa da kai kaya ta jirgin kasa, cewa ya yi layin dogon da shugaban Najeriya Muhamamdu Buhari zai kaddamar zai taimaka wajen kore musu fargaba tare da saukaka musu wajen kashe makudan kudade da zummar safarar kayansu, sabanin yadda suke kashe kudi mai yawa idan da mota ce.

A yayin ziyara da shugaban Buharin zai kawo jahar Kano zai bude gadar sama da kasa dake sha-tale-talen Dangi da ke kan titin zuwa Zariya sannan yaje fadar sarkin Kano, daga bisani ya wuce Katsina inda zai kaddamar da aikin matatar ruwa a karamar hukumar Safana da ke jihar.

Buhari na Kanawa ?

Shugaba Buhari yayin yain neman zaben 2019 a Kano

ASALIN HOTON,KANOGOVT

Bayanan hoto,

Shugaba Buhari yayin yain neman zaben 2019 a Kano

Wasu daga cikin jama'ar jihar dai sun jima suna kokawa a kan yadda suke ganin kamar Shugaba Buhari ya yi watsi da Kano tun bayan hawansa karagar mulki, duk da cewar jihar ta yi ƙaurin suna wajen mara masa bayan tun lokacin da yake takarar shugaban kasa.

Yayin da mulkin shugaban ya taho gangara dai wasu masu shari na ganin cewa dasa harsashin wannan gagarumin aiki daga Kano na nuna kokarin shugaba Buhari na son ganin ya nuna wa jama'ar jihar cewa bai manta da su ba.

A yayin ziyarar shugaban dai ana sa ran zai kaddamar da wasu ayyuka da gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya yi, da suka hadar da gadar sama da kasa dake sha-tale-talen Dangi.

Rahotun BBC Hausa

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN