Da Ɗuminsa: Bayan Komawarsa APC, Gwamna Matawalle Ya Sallami Dukkan Mashawartansa Na Musamman


Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya sallami dukkan mashawartansa na musamman (SA) banda mutum daya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Wannan na ƙunshe ne cikin wani jawabi da sakataren gwamnatin jihar na riƙo kuma shugaban ma'aikata, Alhaji Kabiru Balarabe, ya fitar.

Balarabe yace mai baiwa gwamna shawara ta musamman kan tsaro, Mai ritaya DIG Mamman Tsafe, shine kaɗai wanda zai cigaba da riƙe muƙaminsa.

Wani ɓangaren jawabin yace:

"Muna sanar da al'ummar Zamfara cewa, Gwamna Bello Matawalle, ya sallami dukkan masu ba shi shawara ta musamman daga muƙamansu, amma banda mai bada shawara kan tsaro."

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle

Da Ɗuminsa: Bayan Komawarsa APC, Gwamna Matawalle Ya Sallami Dukkan Mashawartansa Na Musamman Hoto: @bellomatawalle1

Balarabe ya umarci dukkan waɗanda abun ya shafa da su miƙa al'amuran ofisoshinsu zuwa ga daraktocin dake ƙarƙashin su, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Hakanan kuma, Balarabe ya miƙa saƙon godiyar gwamna ga waɗanda wannan mataki ya shafa bisa gudummuwar da suka bada wajen cigaban jihar Zamfara

Gwamna Matawalle yayi haka ne saboda ya koma APC

Gwamna Matawalle na jihar Zamfara ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC a ranar Talata 29 ga watan Yuni.

A cewar Balarabe, gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne saboda ya fice daga PDP ya koma APC.

"Matakin sallamar masu bada shawarar na da alaƙa da sauya sheƙa zuwa APC, domin hakan zai bada damar zaƙulo wasu kwararru waɗanda za'a dama da su a gwamnatin, kuma ba tare da ɗuba banbanci ba." inji Balarabe.

IGP Usman Baba, ya bayyana wa yan majalisar wakilai cewa hukumarsa na aiki ba dare ba rana domin bada tsaro ga yan Najeriya, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Baba ya faɗi haka ne yayin da ya bayyana gaban kwamitin kula da ayyukan hukumar yan sanda ranar Laraba.

Source: Legit.ng

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN