Da dumi-dumi: Shugaban 'yan fashi ya kai hari kauyukan Zamfara, ya sace mutum 150 saboda an kama mahaifinsa


Turji ya kai hare-hare kauyukan Zamfara inda ya sace mutum 150 saboda an kama mahaifinsa Hoto: Governor Bello Matawalle

Legit.ng ta tattaro cewa hare-haren sun fara ne a ranar Juma’a, 16 ga watan Yuli, kuma sunci gaba inda aka yi garkuwa da kimanin mutane 150.

An rahoto cewa jami’an tsaron sun kama mahaifin Turji a cikin garin Kano kimanin makonni biyu da suka gabata kuma tun daga nan ba a san inda yake ba.

Kauyukan da aka kai hari ranar Juma’a:

1. Kurya

2. Keta

3. Kware

4. Badarawa

5. Marisuwa

6. Maberaya, da sauransu

Baya ga fatattakar kauyukan, an rahoto cewa yan bindigan sun kuma sace matafiya da yawa akan hanyar Gusau zuwa Sokoto.

Turji ya lashi takobin hana mutane da yawa jin daɗin Sallah tare da danginsu

An yi zargin cewa Turji ya sha alwashin cewa idan har za a hana mahaifinsa yin Sallah mai zuwa a gida to zai kuma tabbatar da cewa wasu mutane da yawa ba su yi bikin tare da danginsu ba.

Daily Trust ta nakalto wata majiya tana cewa Turji ya yi tir da kamun mahaifinsa. Shugaban 'yan fashin ya ce shi dan ta'adda ne kuma an san wurin da yake, don haka babu dalilin da zai sa a kama mahaifinsa.

Wata majiyar da jaridar ta ambato ta yi ikirarin cewa Turji ya aike da gargaɗi zuwa "ƙauyuka masu ƙawance" yana mai neman su fice.

Wani mazaunin garin Shinkafi, Mohammed Sani, ya yi zargin cewa wani makami mai linzami da aka harba cikin garin ya lalata sassan gidan sarki.

Sai dai kuma, rundunar yan sanda bata tabbatar da ci gaban ba.

A wani labari na daban, wasu yan bindiga da ake zargin fulani ne sun sake kai hari Igangan, ƙaramar hukumar Ibarapa ta arewa, jihar Oyo, da daren ranar Jumu'a, inda duka kashe mutum huɗu, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Sai dai jami'an tsaron sa kai na yankin sun samu nasarar fatattakar maharan kafin su yi mummunar ɓanna.

Kwamandan jami'an tsaron Amotekun a ƙaramar hukumar Ibarapa, wanda aka bayyana sunansa da Muri, ya na daga cikin waɗanda suka rasa ransu.

Source: Legit

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN