Cikakken rahotun shawarwari 10 da Gwamnonin kudu suka yanke kan makomar Najeriya


Ƙungiyar gwamnonin jihohin kudancin Najeriya ta yanke shawara kan matakai daban-daban game da makomar ƙasar a taron da ta gudanar ranar Litinin a birnin Lagos.

A sanarwar da gwamnonin suka fitar, wadda shugabansu Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na jihar Ondo ya sanya wa hannu, sun bayyana goyon bayansu ga kasancewar Najeriya a matsayin ƙasa ɗaya dunƙulalliya.Sun gudanar da taron ne kwanaki kaɗan bayan jami'an hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, sun kai sumame gidan mai fafutukar kafa ƙasar Yarabawan nan Sunday Igboho, inda suka gano manya-manyan makamai.

Hakan na faruwa ne bayan gwamnatin Najeriya ta kamo Mr Nnamdi Kanu, mai rajin ɓallewa daga ƙasar domin kafar ƙasar Biafra.

Wasu na ganin gwagwarmayar da mutanen biyu suke yi tana da nasaba da siyasa kodayake gwamnonin sun yaba kan matakin da gwamnatin tarayya take ɗauka domin wanzar da tsaron a yankin.

'Farin jinin Buhari yana raguwa a tsakanin talakawa'

Ibrahim Shekarau: 'Ya kamata APC ta tsayar da dan takarar shugaban ƙasa daga kudancin Najeriya'

APC da PDP: Wa ce jam'iya ce ta fi kawo koma baya a Najeriya tsakaninsu?

Ga matakan da gwamnonin suka ɗauka game da makomar Najeriya:

Sun ce dole shugabancin Najeriya ya kasance na karɓa-karɓa daga yankin arewaci zuwa kudanci, kuma suna son shugaban ƙasa da za a zaɓa a 2023 ya fito daga yankin kudancin ƙasar saboda abin da gwamnonin suka kira tabbatar da adalci

Gwamnonin kuma sun amince da wasu buƙatu da suke son a aiwatar da suka shafi tsaro da yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima da kuma dokar man fetur.

Sun sake jaddada goyon baya ga haɗin kan Najeriya.

Tabbatar da bukatar ƴan sandan jiha

Dole ne duk wata hukumar tsaro ta nemi izininsu kafin ƙaddamar da samame a jihohinsu

Ƙungiyar gwamnonin ta koka kan yadda a cewarta ake nuna son kai wajen tabbatar da adalci a Najeriya tana mai cewa ya kamata duk wanda za a kama a bi doron doka da 'yancin ɗan ƙasa

Sun tsayar da ranar 1 ga Satumban 2021 da dokar hana kiwo za ta fara aiki a dukkanin jihohin kudanci

Ta yanke shawarar cewa dole a raba kuɗin da ake cirewa daga Asusun Tarayya na Gidauniyar 'yan sanda ta ƙasa tsakanin Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi

Ƙungiyar gwamnonin ta yi fatali da matakin da majalisar dokokin ƙasar ta suka ɗauka na cire aika sakamakon zabe ta hanyar intanet daga dokokin zaben kasar;

Kungiyar kuma ta zaɓi Lagos a matsayin hedikwatar ƙungiyar gwamnonin kudancin Najeriya

Rahotun BBC

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN